Shari'ar Atiku da Buhari: Kotu ta baiwa Buhari damar duba kuri'un da aka jefa

Shari'ar Atiku da Buhari: Kotu ta baiwa Buhari damar duba kuri'un da aka jefa

Kotu ta musamman dake sauraron karar zaben shugaban kasar da aka gudanar watan da ya gabata tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da kuma Shugaba Buhari ta baiwa shugaban damar duba kuri'un da aka kada a zaben.

Wannan hukuncin na kotun dai na zuwa ne biyo bayan bukatar hakan da lauyoyin dake wakiltar bangaren na shugaban kasa a shari'ar da suka shigar a gaban alkalin dake sauraron karar.

Shari'ar Atiku da Buhari: Kotu ta baiwa Buhari damar duba kuri'un da aka jefa
Shari'ar Atiku da Buhari: Kotu ta baiwa Buhari damar duba kuri'un da aka jefa
Asali: Facebook

KU KARANTA: APC ta bayyana yadda zata zabi shugabannin majalisa

Legit.ng Hausa ta samu cewa da suke bayar da hujjojin bukatar su ta samun damar, lauyoyin sun ce suma a matsayin su na masu kare kan su yana da kyau su samu damar duba kuri'un kamar yadda bangaren masu kara na Atiku Abubakar suka bukata.

A wani labarin kuma, Wasu 'yan gari a unguwar Itafaji dake a garin Legas mun samu labarin cewa sun yiwa gwamnan jihar Akinwunmi Ambode ruwan duwatsu yayin da yake barin wurin ginin makarantar nan da ya ruguje da daliban Firamare akalla 80.

Su dai mutanen garin wadanda ke cikin yanayi irin na kaduwa da bakin ciki, sun tattaru a wurin makarantar suna alhini tare da ayyukan ceto sauran yaran da ake tunanin buraguzan gini ya danne su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel