Tura-ta-kai-bango: Wani gwamnan APC ya sha ruwan duwatsu a wurin mafusatan matasa

Tura-ta-kai-bango: Wani gwamnan APC ya sha ruwan duwatsu a wurin mafusatan matasa

Wasu 'yan gari a unguwar Itafaji dake a garin Legas mun samu labarin cewa sun yiwa gwamnan jihar Akinwunmi Ambode ruwan duwatsu yayin da yake barin wurin ginin makarantar nan da ya ruguje da daliban Firamare akalla 80.

Su dai mutanen garin wadanda ke cikin yanayi irin na kaduwa da bakin ciki, sun tattaru a wurin makarantar suna alhini tare da ayyukan ceto sauran yaran da ake tunanin buraguzan gini ya danne su.

Tura-ta-kai-bango: Wani gwamnan APC ya sha ruwan duwatsu a wurin mafusatan matasa
Tura-ta-kai-bango: Wani gwamnan APC ya sha ruwan duwatsu a wurin mafusatan matasa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: An soma daukar aiki a NNPC

Kamar dai yadda wakilin Legit.ng ya tabbatar mana, shima gwamnan jihar ya je jajantawa wadanda ibtila'in ya afkamawa kuma yayin da yake barin wurin sai matasan suka rika jifar tawagar sa.

Su dai mutanen unguwar suna jin haushin gwamnatin jihar ne bisa rugujewar ginin musamman ma ganin cewa tuni gwamnatin jihar tayi wa ginin alamar rushewa amma sai taki yin hakan.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ba rukunin kamfanonin albarkatun mai na Najeriya watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) umurnin kwace lasisin rijiyar mai mai lamba Oil Mining Lease 11 (OML 11) daga hannun kamfanin Shell.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata takardar umurni daga fadar shugaban kasar zuwa ga kamfanin na NNPC mai dauke da kwanan wata 1 ga watan Maris, da kuma lambar ofis ta SH/COS/24/A/8540 dauke da sa hannun shugaban ma'aikata, Abba Kyari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel