Okorocha ya daura laifin faduwar da APC tayi a kudu maso gabas akan Oshiomole da Uzodimma

Okorocha ya daura laifin faduwar da APC tayi a kudu maso gabas akan Oshiomole da Uzodimma

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya bayyana cewa Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Missta Adams Oshiomhole, da kuma dan takarar gwamnan jam’iyyar Hope Uzodimma ne suka yi sanadiyar rashin lashe zaben gwamna da jam’iyyar bata yi ba a jihar.

Yace zuriyyarsu na nan gaba za su daura alhakki akan shugabannin biyu sakamakon rawar ganin da suka taka a zaben.

Okorocha ya daura laifin faduwar da APC tayi a kudu maso gabas akan Oshiomole da Uzodimma
Okorocha ya daura laifin faduwar da APC tayi a kudu maso gabas akan Oshiomole da Uzodimma
Asali: UGC

A wani jawabi da babban sakataren labaransa, Mista Sam Onwuemeodo ya saki a Owerri a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris gwamnan yayi zargin cewa Uzodinma nayiwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) aiki a zaben da aka kammala.

Yace Uzodimma ne mutum na farko da ya fara taya dan takarar PDP, Cif Emeka Ihedioha murna bayan an kaddamar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben, inda yayi nuni ga wani bidiyon yan takarar biyu a matsayin tabaci ga hakan.

A wani lamari na daban, Legit.g ta rahoto cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zargi gwamnatin tarayya da kuma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da shirin yin amfani da sojoji da sauaran hukumomin tsaro wajen lashe jihar Sokoto ta karfi da yaji.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta zargi Galadima da Timi Frank da yada labaran karya

Hukumar zabe mai zaman kantan (EFCC) ta shirya sake gudanar da zabe a jihar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, biyo bayan ikirarin cewa ba a gane wanda ya lashe zabe ba a zaben farko da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel