Tazarcen Buhari: FG ta kafa kwamitin rantsar da shugaban kasa

Tazarcen Buhari: FG ta kafa kwamitin rantsar da shugaban kasa

Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya bukaci mambobin kwamitin rantsar da shugaban kasa da su zage dantse domin ganin an yi rantsuwar shugaban kasa cikin nasara.

Mustapha ya yi wannan kira ne yau, Alhamis, a Abuja yayin rantsar da mambobin kwamitin.

Ya bukaci mambobin kwamitin da su yi amfani da gogewar da suke da ita yayin gudanar da aikin su.

Ya kara da cewar kwamitin zai kafa wasu kananan kwamitin da ministoci zasu jagoranta.

A cewar Mustapha, kwamitin zai zabo Karin wasu mambobi daga jam’iyyar APC domin tabbatar da daidaito.

Ya ce wadanda za a zaba daga jam’iyyar APC zasu kasance mambobi ne a kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari da kuma wasu kungiyoyin goyon bayan sa.

Tazarcen Buhari: FG ta kafa kwamitin rantsar da shugaban kasa
FG ta kafa kwamitin rantsar da shugaban kasa
Asali: Twitter

Tazarcen Buhari: FG ta kafa kwamitin rantsar da shugaban kasa
Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin rantsar da shugaban kasa
Asali: Twitter

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar shugaba Buhari ya amince da kafa kwamitin karkashin jagorancin SGF.

Babbar sakataren harkokin siyasa da tattalin arziki a ofishin SGF zai kasance sakataren kwamitin.

DUBA WANNAN: Fitar da N233m: KASCISSIR ta rubuta korafi zuwa ga EFCC a kan Ganduje

Mambobin kwamitin su ne: ministan yada labara da al’adu, ministan harkokin gida, ministan harkokin kasashen waje, da na birnin tarayya.

Ragowar su ne; ministan tsaro, na lafiya, na ilimi, na bangaren filyaen jirgim sama, shugaban jam’iyyar APC da babban sifeton rundunar ‘yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel