Sake zabe: PDP ta zargi gwamnatin tarayya da shirin lashe Sokoto ta karfi da yaji

Sake zabe: PDP ta zargi gwamnatin tarayya da shirin lashe Sokoto ta karfi da yaji

- Jam' iyyar PDP ta zargi gwamnatin tarayya da kuma jam’iyyar APC da shirin yin amfani da sojoji da sauaran hukumomin tsaro wajen lashe jihar ta karfi da yaji

- Hukumar zabe mai zaman kantan (EFCC) ta shirya sake gudanar da zabe a jihar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris

- PDP ta bayyana cewa duk wani yunkuri na gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro wajen ganin sun yi magudi a gudanarwar sai haifar da illar mai tsanani

Ana saura kwanki goma a sake zaben gwamna a jihar Sokoto, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zargi gwamnatin tarayya da kuma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da shirin yin amfani da sojoji da sauaran hukumomin tsaro wajen lashe jihar ta karfi da yaji.

Hukumar zabe mai zaman kantan (EFCC) ta shirya sake gudanar da zabe a jihar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, biyo bayan ikirarin cewa ba a gane wanda ya lashe zabe ba a zaben farko da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris.

Sake zabe: PDP ta zargi gwamnatin tarayya shirin lashe Sokoto ta karfi da yaji
Sake zabe: PDP ta zargi gwamnatin tarayya shirin lashe Sokoto ta karfi da yaji
Asali: Twitter

Amma sai PDP, wanda a inuwarta ne gwamna Aminu WaziriTambuwal yayi takara ta yi wani kakkausar gargadi a ranar Alhamis akan gwamnatin tarayya da jam’iyyar adawa ta APC a Sokoto da jkada su yi amfani da dole wajen murkushe burin masu zabe a Sokoto.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta zargi Galadima da Timi Frank da yada labaran karya

A wani jawabi da Shugaban PDP a Sokoto, Alhaji Ibrahim Milgoma ya gabatar ga manema labarai jam’iyyar ta bayyana cewa duk wani yunkuri na gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro wajen ganin sun yi magudi a gudanarwar sai haifar da illar mai tsanani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel