Fitar da N233m: KASCISSIR ta rubuta korafi zuwa ga EFCC a kan Ganduje

Fitar da N233m: KASCISSIR ta rubuta korafi zuwa ga EFCC a kan Ganduje

Wata kungiya mai rajin kare hakkin jama’ar jihar Kano (KASCISSIR) ta rubuta takardar korafi zuwa ga hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) a kan zargin gwamnatin jihar Kano da fitar da kudi miliyan N233 domin sayen kuri’u a zaben gwamna da za maimaita a wasu mazabu a jihar a ranar 23 ga watan Maris.

A takardar korafin, mai dauke da sa hannun 14 ga watan Maris, da majiyar mu ta gani, KASCISSIR ta bayyana cewar an fitar da makudan kudin ne daga asusun jihar Kano ta hannun ma’aikatar kula da kananan hukumomi.

Kungiyar ta yi zargin cewar gwamnatin jihar Kano ta kasafta kudin zuwa kaso 30, adadin kananan hukumomin da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewar za a maimaita zabe a wasu mazabunsu.

“Mun samu bayani a kan fitar da kudin tun ranar 12 ga watan Maris, 2019. Dadi da kari, a ranar 13 ga watan Maris, sai ga shi an kama wasu wakila APC da su ka amsa da bakinsu a shirin ‘In da ranka’ na gidan radiyon Freedom cewar su na yiwa jam’iyyar aikin sayen kuri’a ne.

Muna fata hukumar EFCC zata yi bincike a kan wannan korafi tare da daukan matakan ganin cewar ba a yi amfani da kudaden wajen sayen kuri’a kafin ko a lokacin zabe,” a cewar KASCISSIR.

Fitar da N233m: KASCISSIR ta rubuta korafi zuwa ga EFCC a kan Ganduje
Ganduje
Asali: Twitter

Sai dai, da aka tuntubi kwamishinan kananan hukumomin jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya yi watsi da zargin cewar an fitar da kudin ne domin sayen kuri’u.

Tabbas an fitar da kudin kuma an raba su zuwa kananan hukumomi 13 domin kaddamar da wasu aiyuka. Idan aka duba kananan hukumomin da za su ci moriyar kudin za a fahimci cewar zargin da was ke yi bashi da tushe balle makama.

DUBA WANNAN: Manufar maimaita zabe a wajen ‘yan takarar jam’iyyar APC – Sanata Shehu Sani

“Kananan hukumomin Kumbotso, Kabo, Dawakin Tofa da Tsanyawa na daga cikin kananan hukumomin da su ka samu kaso mai tsoka daga cikin kudin kuma basa cikin wadanda za a maimaita zabe.

“Idan da gaske ne kudin na sayen kuri’a ne da sai mu raba su a tsakanin kananan hukumomi 30 da za a maimaita zabe a wasu daga cikin mazabunsu,” a cewar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel