Rundunar soji ta zargi Galadima da Timi Frank da yada labaran karya

Rundunar soji ta zargi Galadima da Timi Frank da yada labaran karya

Rundunar sojin Najeriya ta nada tsohon mataimakin sakataren jam’iyyar APC na kasa, Timi Frank da Shugaban kungiyar sabuwar APC (R-APC), Buba Galadima a matsayin yan Najeriya masu yada labaran karya.

A wani rubutu da rundunar sojin ta wallafa a shafin twitter a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris ta bayyana Frank da Galadima a matsayin iyayen watsa labaran karya.

rundunar sojin ta bukaci jama’a da kada su yada bayan karya daga Frank da Galadima.

“Wadannan ne fuskokin yan Najeriya masu yada labaran karya. Ana umurtanku da kada ku yada bayanansu na karya.”

A wani labari na daban, mun ji cewa Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi martani ga zargin mutuwar direbansa da kuma rahoton cewa yana cikin wani yanayi, inda ya bayyana hakan a matsayin aikin makiya masu adawa da shi a jihar.

KU KARANTA KUMA: Manufar maimaita zabe a wajen ‘yan takarar jam’iyyar APC – Sanata Shehu Sani

Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan ya rubuta a shafinsa na Facebook mai suna Nasir El-Rufai a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris cewa labarin karya da kuma tunanin magauta.

El-Rufai ya kaddamar da cewa bai yi mamakin labarin ba, inda ya kara da cewa ya kasance dodon yan PDP da makiyansa a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel