Yanzu Yanzu: El-Rufai ya yi martani ga jita-jitan mutuwarsa

Yanzu Yanzu: El-Rufai ya yi martani ga jita-jitan mutuwarsa

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi martani ga zargin mutuwar direbansa da kuma rahoton cewa yana cikin wani yanayi, inda ya bayyana hakan a matsayin aikin makiya masu adawa da shi a jihar.

Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan ya rubuta a shafinsa na Facebook – Nasir El-Rufai a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris cewa labarin karya da kuma tunanin magauta.

El-Rufai ya kaddamar da cewa bai yi mamakin labarin ba, inda ya kara da cewa ya kasance dodon yan PDP da makiyansa a jihar.

Yanzu Yanzu: El-Rufai ya yi martani ga jita-jitan mutuwarsa
Yanzu Yanzu: El-Rufai ya yi martani ga jita-jitan mutuwarsa
Asali: UGC

Yace: “Na tashi bayan baccin sa’oí-8 sai naji cewa an shirya wani kagaggen labarai, labarin karya da aka kaddamar cewa direba na ya mutu sannan cewa nima ina cikin wani hali.

KU KARANTA KUMA: Zaben shugaban kasa: Buhari ya bukaci kotu da ta bada damar binkicen kayan zabe

“Dukkanin ikirarin karya ne. Ina godiya gare su da suka rage ma kansu kwanaki sannan suke kara mun akan nawa. Har gobe nine dodonsu."

A wani lamari na daban, mun ji cewa Shehu Sani, Sanata mai barin gwado daga mazabar jihar Kaduna ta tsakiya, ya bayyana cewar an kirkiri maimaita zabe a wasu jihohi ne domin bawa ‘yan takarar APC damar cin zabe.

A cewar sanatan, “maimaita zaben tamkar sake rubuta jarrabawa ne ga ‘ya’yan jam’iyya mai mulki.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel