Zaben da za a sake a Kano na 'ko a mutu-ko a yi rai' ne: An bukaci a kama shugaban APC

Zaben da za a sake a Kano na 'ko a mutu-ko a yi rai' ne: An bukaci a kama shugaban APC

Cibiyar fasahar sadarwa da cigaba CITAD ta bukaci a kama shugaban jam'yyar APC na jihar Kano, Alhaji Abbas saboda wasu kalaman harzuka al'umma da ya fadawa magoya bayansa gabanin zaben gwamna da za a maimaita.

Shugaban sashin kawar da kalaman kiyaya na CITAD, Malam Hamza Ibrahim ne ya yi wannan kirar a jiya cikin wata hirar wayan tarho da ya yi da Daily Trust bayan ya fitar da sanarwar jan hankalin jami'an tsaro a kan kalaman kiyayar da shugaban na APC ya yi.

Idan ba a manta ba a ranar Litinin, Hukumar INEC ta sanar da cewa zaben jihar Kano bai kammala ba saboda haka ta sake zaben sabuwar ranar da za a maimaita zaben a wasu mazabu 172 a kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

DUBA WANNAN: APC 13, PDP 9: Jerin sunayen sabbin gwamnoni da INEC ta sanar sun lashe zabe

Zaben da za a sake a Kano na 'ko a mutu-ko a yi rai' ne - Shugaban APC
Zaben da za a sake a Kano na 'ko a mutu-ko a yi rai' ne - Shugaban APC
Asali: Facebook

Hamza ya tunatar da hukumomin tsaro da su kasance masu daukan mataki a kan al'amurra domin kare afkuwar fitina da kuma hukunta masu yada kalaman kiyayar domin zama darasi a kan wasu.

A sanarwar da CITAD ta fitar a kan faifan bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta inda aka gano shugaban na APC yana fatawa wasu magoya bayansa cewa su tabbatar jam'iyyar APC tayi nasara ko da tsiya ko da arziki.

Ibrahim ya ce kalaman da suka fito bakin Abbas abin damuwa ne a jihar da kuma demokradiyar Najeriya.

"A matsayin mu na cibiyar mai tabbatar da zaman lafiya, CITAD tana matukar damuwa a kan wannan lamarin. Abin damuwa ne yadda aka gano shugaban APC, Hon. Abdullahi Abbas a faifan bidiyo yana tunzura matasa su tayar da hankula a zaben da ke tafe.

"Kalaman abin tsoro ne musamman yadda ya bawa matasan lasisin dukan duk wanda suka ga dama saboda a cewarsa ba za su bari 'yan sanda da sojoji suyi musu komai ba."

Ibrahim ya kuma shawarci matasa su fahimci cewa ana kyautata zaton ba za su bari ayi amfani da su wurin tayar da hankali ba yayin zabe da ma bayan zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel