Manufar maimaita zabe a wajen ‘yan takarar jam’iyyar APC – Sanata Shehu Sani

Manufar maimaita zabe a wajen ‘yan takarar jam’iyyar APC – Sanata Shehu Sani

Shehu Sani, Sanata mai barin gwado daga mazabar jihar Kaduna ta tsakiya, ya bayyana cewar an kirkiri maimaita zabe a wasu jihohi ne domin bawa ‘yan takarar APC damar cin zabe.

A cewar sanatan, “maimaita zaben tamkar sake rubuta jarrabawa ne ga ‘ya’yan jam’iyya mai mulki.”

Shehu Sani ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutaccen sako da ya fitar a shafinsa na Tuwita a jiya, Laraba, 13 ga watan Maris.

Sanatan ya kara wallafa wani rubutun da safiyar yau, Alhamis, inda ya zargi gwamnotin baya da gwamnati mai ci da kin mayar da hankali wajen kawo canji a harkar gudanar zabuka a kasar nan.

Ya kara da cewa, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne kadai ya yi wani katabus wajen kawo gyara a harkar gudanar da zabuka a Najeriya, tare da bayyana cewar gyaran da ya kawo shine ya zama silar faduwar sa a zaben shekarar 2015.

Manufar maimaita zabe a wajen ‘yan takarar jam’iyyar APC – Sanata Shehu Sani
Sanata Shehu Sani
Asali: Twitter

Sanata Shehu Sani na daga cikin mambobin majalisar dattijai 64 da su ka fadi zabe a mazabunsu, sai dai ya ce shine ya lashe zaben kujerar sanatan jihar Kaduna ta tsakiya amma aka yi ma sa fashi.

DUBA WANNAN: ‘Yan Kwankwasiyya ba su kori Ganduje daga gidan gwamnati ba – Hadimin Ganduje

Ya bayyana hakan ne yayin hira da aka yi da shi a yau a wani shirin gidan Talabiin din Channels mai taken ‘Politics Today’. Ya ce an kayar da shi zabe ne saboda rashin bin dokokin zabe a mazabu.

Da an gudanar da zabe na gaskiya da b azan fadi ba. Zaben Najeriya a biyu ya ke; ko ka yi fashin nasara, ko kuma a yi maka fashin nasara, sai na yi rashin sa’a ni aka yiwa fashin wannan karon,” a cewar Sanata Shehu Sani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel