Zaben shugaban kasa: Buhari ya bukaci kotu da ta bada damar binkicen kayan zabe

Zaben shugaban kasa: Buhari ya bukaci kotu da ta bada damar binkicen kayan zabe

- Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci kotun sauraron karar zaben Shugaban kasa da ta bada damar binciken kayayyaki da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu

- Buhari ya gabatar da bukatar ne a ranar Alhamis ta hannun lawyan sa wanda Wole Olanipekun (SAN) ya jagoranta

- Bukatar ta kasance iri guda da bukatar dan takaran jam’iyyar PDP a zaben Shugaban kasa, Atiku Abubakar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci kotun sauraron karar zaben Shugaban kasa wato Presidential Election Petitions Tribunal (PEPT) da ke zama a kotun daukaka kara, a Abuja da ta bada damar binciken kayayyaki da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu.

Shugaban kasa Buhari ya gabatar da bukatar ne a ranar Alhamis ta hannun lawyan sa wanda Wole Olanipekun (SAN) ya jagoranta.

Zaben shugaban kasa: Buhari ya bukaci kotu da ta bada damar binkicen kayan zabe
Zaben shugaban kasa: Buhari ya bukaci kotu da ta bada damar binkicen kayan zabe
Asali: Facebook

Rubutacciyar bukatar wanda yake da goyon bayan sashi na 151 (1) da (2) na tsarin zabe, tana bukatar kotun daukaka kara da ta tilasta INEC damar binciken takardu don samun shaidu kan harkokin zabe.

Bukatar ta kasance iri guda da bukatar dan takaran jam’iyyar PDP a zaben Shugaban kasa, Atiku Abubakar, na son a tilasta wa INEC gabatar da rijistan masu zabe, na’urar dake tantance kati, takardun zabe, da duk sauran kayayyaki masu muhimmanci don bincike.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Osinbajo, Bindow da Abubakar sun yi ganawar sirri a Aso Rock

Kotu ta gabatar da rubutacciyar bukatar ne a ranar 6 ga watan Maris.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel