Dakarun Soji sun kara samun nasara kan yan Boko Haram

Dakarun Soji sun kara samun nasara kan yan Boko Haram

Dakarun sojin Najeriya sun kara samun wani gagarumin nasara kan yan kungiyar ta'addan Boko Haram dake addaban yankin Chadi, arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin rundunar sojin kasa da kasa wato Multinational Joint Task Force (MNJTF), Kanal Timothy Antigha, ya saki jawabin irin asarar da jami'an rundunar suka yiwa yan Boko Haram a kwanaki biyu da suka gabata.

A jawabin da ya saki yace: "Bisa ga shirin da rundunar sojin kasa da kasa tayi na ragargaza yan Boko Haram da tayar dasu daga tafkin Chadi, rundunar sojin sama da kasa sun zange dantse wajen wargaza su."

A wata arangama, sashen leken asiri da jami'an sojin kasa tare da hadin kan sojin kasashen Kamaru da Nijar sun tarwatsa yan Boko Haram a Tunbum Rogo, wata tsibiri dake tafkin Chadi, da Boko Haram ta shahara da shi."

KU KARANTA: Kwankwaso ya umurci Abba Gida-gida kada ya biya mafi karancin albashi N30,000

Bugu a kari, jami'an MNJTF daga Sakta 4 sun aki hari mabuyar Boko Haram dake Arege ida suka hallaka yan ta'addan kuma suka kwato makamai, ga jerin makaman da suka kwato:

1. An kashe yan Boko Haram 33

2. An kwato Motacin yaki biyu

3. An lalata wata tankar yaki

4. An lalata babura biyu

5. An kwato 120MM daya

6. An kwato bindigar AK47 12

7. An kwato bama-bamain 60MM biyu.

8. An kwato carbin harsasai 3736

9. An kwato wata na'urar hangen nesa

10. An kwato gurnet biyu

Dakarun Soji sun kara samun nasara kan yan Boko Haram
Dakarun Soji sun kara samun nasara kan yan Boko Haram
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel