Dino Melaye yace Buhari ya aro fiye da Dala Biliyan 40 a cikin shekaru 3

Dino Melaye yace Buhari ya aro fiye da Dala Biliyan 40 a cikin shekaru 3

- Sanatoci sun samu sabani game da tarin bashin da ke kan wuyan Najeriya

- Dino Melaye yace shugaba Buhari ya tattarowa Najeriya makukun bashi

-‘Yan Majalisan kasar sun yi kira ga Gwamnati ta bi sannu wajen aron kudi

An samu surutu a majalisar dattawan tarayya a jiya Laraba 13 ga Watan nan na Maris. Batun tarin bashin da ke kan Najeriya ne ya jawo wannan hayaniya. Sanata Dino Melaye yake cewa bashin kasar nan ya karu sosai a yanzu.

Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Ike Ekweremadu, yace dole gwamnatin tarayya ta bi a sannu wajen cin bashi. Dino Melaye yace a lokacin da PDP ta ajiye mulki a 2015, bashin da ke kan kasar bai wuce fam Dala biliyan 20 ba.

An kawo wannan magana ne bayan da Sanata Ahmad Lawan ya tado da maganar kasafin kudin bana. Mataimakin shugaban majalisar yace ya kamata gwamnati ta sake gano hanyar samun kudin yin aikace-aikace ba tare da bashi ba.

KU KARANTA: Majalisa ta amince da biyan karancin albashin N30,000 a Najeriya

Dino Melaye yace Buhari ya aro fiye da Dala Biliyan 40 a cikin shekaru 3
Sanata Dino Melaye ya fadawa Gwamnatin Tarayya ta bi sannu da cin bashi
Asali: UGC

Dino Melaye, wanda shi ne ‘Dan majalisar dattawa mai wakiltar yankin Kogi ta yama a karkashin PDPya bayyana cewa bashin da ake bin Najeriya ya haura Dala biliyan 60. Melaye yace bashin ya hauhawa ne a lokacin mulkin APC.

Sanata Dino Melaye yace irin bashin da gwamnatin Buhari ta ke karbowa da sunan gina abubuwan more rayuwa ya soma yin yawa. Melaye yace dole a bi hankali ganin yadda abubuwa su kayi tsada da kuma rashin aikin yi da yayi yawa.

‘Yan Majalisa da-dama irin su Shehu Sani, da kuma Albert Akpan Bassey sun goyi bayan Dino Melaye. Sai dai Sanatocin APC irin su Gbenga Ashafa, Adamu Aliero, da Jibrin Barau da kuma Sanata Bala Ibn Na’Allah sun yi watsi da maganar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel