Da dumi dumi: Majalisar dattawa ta amince da biyan karancin albashin N30,000 ga ma’aikata

Da dumi dumi: Majalisar dattawa ta amince da biyan karancin albashin N30,000 ga ma’aikata

Majalisar dattawa ta amince ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya biya ma’aikatan Najeriya karancin albashin naira dubu Talatin, N30,000, kamar yadda takwararta, majalisar wakilai ta amince tun a watan Janairu.

Legit.ng ta ruwaito Sanata Shehu Sani ne ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, inda ya daura hotunan yayan kwamitin tattauna dokar karancin albashin a lokacin da suke karkare tattaunawa akan lamarin.

KU KARANTA: Koda tsiya tsiya sai mun ci zaben nan – shugaban APC ta Kano

Da dumi dumi: Majalisar dattawa ta amince da biyan karancin albashin N30,000 ga ma’aikata
Yan kwamitin
Asali: UGC

Kwamitin na karkashin jagorancin mataimakin bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Francis Alimikhena na jam’iyyar APC ne, sauran mambobin kwamitin sun hada da Shehu Sani, Sanata Abu Ibrahim, Sanata Sam Egwu, Sanata Solomon Adeola, Sanata Binta Garba da kuma Sanata Suleiman Adokwe.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a yayin zaman karshe na tattauna dokar samar da karancin albashin, dukkanin mambobin kwamitin sun bayyana amincewarsu dari bisa dari game da biyan wannan kudi, har ma suka sanya tarar N75,000 ga duk ma’aikacin da aka kama bai je aiki ba.

Ana sa ran kwamitin zata mika cikakken rahotonta ga majalisar a ranar Talata na makon gobe. Shima guda daga cikin mambobin kwamitin, Sanata Adeola ya bayyana cewa sun amince da 30,000 amma akwai bukatar gwamnatocin jahohi da na kananan hukumomi su dabbaka dokar suma.

Don haka Sanata Adeola yayi kira ga hukumar rarraba arzikin kasa data gaggauta duba tsarin yadda take raba kudade ga gwamnatin tarayya, jahohi da kananan hukumomi don kowannensu ya samu damar biyan wanann kudi kamar yadda majalisar ta tabbatar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel