Yanzu Yanzu: Osinbajo, Bindow da Abubakar sun yi ganawar sirri a Aso Rock

Yanzu Yanzu: Osinbajo, Bindow da Abubakar sun yi ganawar sirri a Aso Rock

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo sun yi ganawar sirri da gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar da kuma takwaransa na jihar Adamawa, Jibrilla Bindow a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Gwamnonin biyu na neman tazarce a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Sai dai an kaddamar da zaben gwamnoni da aka gudanar a jiohin biyu a ranar Asabar, 9 ga watan Maris a matsayin ba kammalallu ba.

Yanzu Yanzu: Osinbajo, Bindow da Abubakar sun yi ganawar sirri a Aso Rock
Yanzu Yanzu: Osinbajo, Bindow da Abubakar sun yi ganawar sirri a Aso Rock
Asali: Facebook

Zuwa yanzu dai ba a sanar da abunda ganawar tasu ta kunsa ba a daidaiu lokacin kawo wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Mawaki Naziru ya roki Buhari ka da ya bari a murde zaben Kano

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa wata babbar kotun jiha da ke da zama a Yola ta bayar da wani umurni da ke dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta daga sake gudanar da zaben gwamna a jihar Adamawa.

Justis Abdulaziz Waziri na kotun jihar ya bayar da wannan umurni ne bio bayan wata kara da jam’iyyar Movement of Restoration for Defence of Democracy (MRPD), ta shigar wanda ke ikirarin cewa an cire logon jam’iyyarta daga takardar zaben gwamna day a gudana a ranar 9 ga watan Maris.

An kuma tattaro cewa a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zargi Gwamna Jibrilla Bindow da shirin amfani da MRPD wajen juya zaben da za a sake gudanarwa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel