Sake zabe: Ni zan yi nasara a jihar Kano - Gwamna Ganduje

Sake zabe: Ni zan yi nasara a jihar Kano - Gwamna Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya jaddada ikirarin cewa jam'iyyar sa ta APC za ta yi nasara a yayin sake zaben gwamna a wasu rumfuna da mazabu da ke fadin jihar Kano da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta kayyade.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta yanke hukuncin sake zaben gwamna a ranar 23 ga watan Maris cikin wasu rumfuna da mazabu na jihar Kano a sakamakon rashin kammalar zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Sake zabe: Ni zan yi nasara a jihar Kano - Gwamna Ganduje
Sake zabe: Ni zan yi nasara a jihar Kano - Gwamna Ganduje
Asali: Twitter

Gwamna Ganduje cikin bugun gaba da kuma yakini ya yi ikirarin samun nasara a yayin sake zaben da za a gudanar cikin wasu kananan hukumomi na jihar Kano kamar yadda hukumar INEC da sanadin babban Baturen zabe na jihar, Farfesa Riskuwa Shehu ya tabbatar.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Ganduje ya bayyana hakan yayin wani jawabi da ya gabatar a gaban dandazon magoya bayan sa yayin yi masa lale maraba wajen wata ziyarar aiki da Yini guda da ya kai garin Abuja.

KARANTA KUMA: Buhari ya yi amanna ta fidda €64.75m domin aikin ruwa a jihar Kano

Ganduje ya bayyana farin cikin sa kwarai da aniyya dangane da yadda aka gudanar da zaben gwamna a jihar Kano cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali al'umma ba tare da hargitsi ko tashin-tashina ba.

Ya tabbatar da yakinin samun nasara ga al'ummar jihar Kano yayin sake zaben a ranar Asabar. Ya yi kira da su fito kwansu da kwarkwata wajen kada kuri'u domin tabbatar da 'yancin su da kundin tsarin mulkin kasa ya yi ma su tanadi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel