Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da INEC daga sake gudanar da zaben gwamna a Adamawa

Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da INEC daga sake gudanar da zaben gwamna a Adamawa

Wata babbar kotun jiha da ke da zama a Yola ta bayar da wani umurni da ke dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta daga sake gudanar da zaben gwamna a jihar Adamawa.

Justis Abdulaziz Waziri na kotun jihar ya bayar da wannan umurni ne bio bayan wata kara da jam’iyyar Movement of Restoration for Defence of Democracy (MRPD), ta shigar wanda ke ikirarin cewa an cire logon jam’iyyarta daga takardar zaben gwamna day a gudana a ranar 9 ga watan Maris.

Sai dai wani lauya, Sunday Wugiri ya fada ma jaridar Sahara Reporters cewa “koda dai wannan umurnin na da inganci a yanzu, kotu bata da hurumin gabatar da shi."

Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da INEC daga sake gudanar da zaben gwamna a Adamawa
Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da INEC daga sake gudanar da zaben gwamna a Adamawa
Asali: Original

An kuma tattaro cewa a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zargi Gwamna Jibrilla Bindow da shirin amfani da MRPD wajen juya zaben da za a sake gudanarwa.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce jami'anta sun damke wasu mutane uku da ake zargi da sayan katin zabe daga hannun mutane domin yin magudi a zaben gwamna da za a maimaita a wasu sassan jihar.

KU KARANTA KUMA: Ko sama ko kasa babu sunan Okorocha yayinda zababbun sanatoci ke karban takardar shaida

Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna ne ya bayar da wannan sanarwar a jiya inda ya ce wadanda aka kama sun hada da Sa'adatu Isma'il mai shekaru 39 da ke zaune a Brigade Quaters da Halima Abba mai shekaru 55 da ke zaune a Tal'udu Quaters.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel