Ko sama ko kasa babu sunan Okorocha yayinda zababbun sanatoci ke karban takardar shaida

Ko sama ko kasa babu sunan Okorocha yayinda zababbun sanatoci ke karban takardar shaida

- Ba gano sunan gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ba cikin wadanda hukumar INEC ta bai wa takardar shaidan cin zabe ba

- An tattaro cewa Okorocha ya lashe zaben daya daga cikin kujerun sanatoci na jihar Imo

- A yau ne dai hukumar zaben ta rarrabawa sanatoci da yan majalisar dokokin kasa takardun shidar cin zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta tsaya kaifi daya akan maganarta ta hanyar kin tabbatar da zaben Rochas Okorocha zuwa majalisar dattawa.

Ko sama ko kasa ba a ga sunan gwamnan jihar Imo ba a cikin sunayen zababbun yan majalisar dattawa da suka amshi takardar shaidar zabensu a cibiyar taron kasa-da-kasa a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris.

Ko sama ko kasa babu sunan Okorocha yayinda zababbun sanatoci ke karban takardar shaida
Ko sama ko kasa babu sunan Okorocha yayinda zababbun sanatoci ke karban takardar shaida
Asali: UGC

An tattaro cewa Okorocha ya lashe zaben daya daga cikin kujerun sanatoci na jihar Imo. Sai dai INEC ta takunkumi akan nasarar nasa a zaben.

Da farko Legit.ng ta rahoto cewa a yau Alhamis 14 ga watan Maris ake sa ran hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC za ta raba takardun shaidar cin zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabreru ga mambobin majalisar tarayya, a dakin taro na kasa (ICC) da ke Abuja.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da INEC daga sake gudanar da zaben gwamna a Adamawa

A cewar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, sanatoci 102 ne za su samu takardun shaidar cin zabensu da misalin karfe 10 na safiya, yayin da 'yan majalisun wakilan tarayya 338 za su samu takardunsu da misalin karfe 2 na rana.

Idan aka yi bitar 'yan majalisun tarayyar da suka samu nasara, jam'iyyar APC na da sanatoci 63, jam'iyyar PDP na da 38 ya yin da jam'iyyar YFP ke da kujera daya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel