Buhari ya yi amanna ta fidda €64.75m domin aikin ruwa a jihar Kano

Buhari ya yi amanna ta fidda €64.75m domin aikin ruwa a jihar Kano

A jiya Laraba gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta yi amanna ta malalar da zunzurutun dukiya kimanin €64.75m domin gudanar da wani muhimmin aiki na ruwa a jihar Kano.

Ministan kudi Hajiya Zainab Ahmad, ta bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zantarwa da shugaban kasa Buhari ya jagoranci zaman sa cikin fadar Villa da ke garin Abuja.

Ministar kudin ta ce wannan katafaren aiki da gwamnatin tarayya za ta aiwatar a karkashin gudanarwa da kuma kulawa ta gwamnatin jihar Kano zai yi tasirin gaske wajen inganta rayuwar al'umma baki daya.

Buhari yayin jagorancin zaman majalisar zantarwa
Buhari yayin jagorancin zaman majalisar zantarwa
Asali: Facebook

Cikin kalaman ta Hajiya Zainab ta ce, wannan katafaren aiki zai inganta jin dadin rayuwar al'umma kimanin miliyan 1.5 da ke cikin birnin Kano ta hanyar samar da nagartaccen ruwan sha da kuma gudanar da ayyukan yau da kullum a muhallai da masana'antu.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kimanin Ministoci 28 sun halarci zaman na majalisar zantarwa da ya kasance na farko tun bayan babban zaben kasa na gwamnatin tarayya da kuma na jihohin kasar nan.

KARANTA KUMA: Kasashen Afirka ta Yamma za su fara amfani da samfurin kudi na bai daya a 2020 - ECOWAS

Cikin wadanda suka halarci zaman majalisar a jiya Laraba sun hadar da; Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma'aikatan shugaban kasa Buhari, Abba Kyari, shugaban ma'aikatan gwamnati ta kasa, Winifred Oyo-Ita da kuma babban mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Babagana Monguno.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel