Shugabancin majalisa: Shin Sanatocin APC sun yanke shawara kan Ahmad Lawan?

Shugabancin majalisa: Shin Sanatocin APC sun yanke shawara kan Ahmad Lawan?

An samu manyan alamu da ke nuna cewa sabbin sanatoci da tsaffin da suka samu nasara a zaben karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun yanke shawara kan Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda zasu zaba sabon shugaban majalisar dattawa.

Sun yanke wannan shawara ne saboda irin kwarewar da Ahmed Lawan ya samu kasancewarsa wanda yake majalisar dokokin tarayya tun 1999 fari daga majalisar wakilai sannan na dattawa.

Kana, an samu labarin cewa fadar shugaban kasa na son Ahmed Lawan bisa ga biyayyansa ga jam'iyya da kuma yadda aka so ya zama shugaban jam'iyyar a 2015 amma bai samu ba saboda wasu yan jam'iyyar sun zagaya baya da yan jam'iyyar adawa.

KU KARANTA: ‘Dana ya nemi inyi masa addu’a kafin ya fita – Mahaifin wani yaro da ya mutu a rushewar gini

Kakakin jam'iyyar APC, Malam Lanre Isa Onilu ya bayyanawa jaridar Daily Sun cewa jam'iyyar bata yanke shawara kan hakan ba har sai kwamitin gudanarwa da kwamitin zantarwa kadai zasu iya yanke wannan shawara kuma bau zanna ba har yanzu.

Sanata Ahmed Lawan dan jihar Yobe ne kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa a yanzu.

Akwai wasu manyan yan takaran kujeran daga yankin Arewa maso gabas. Sanata Ali Ndume da Sanata Danjuma Goje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel