Hukumar EFCC ta sake gurfanar da hadimin Saraki, Makanjuola da sauran su

Hukumar EFCC ta sake gurfanar da hadimin Saraki, Makanjuola da sauran su

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) a jiya ta sake gurfanar da Gbenga Makanjuola, mataimakin shugaban ma’aikatan shugaban majalisan dattijai, Bukola Saraki, da sauran su a gaban Justis Maireen Onyetenu da ke babbar kotun Lagas.

An sake gurfanar da su ne bisa zargin hadin baki, karban wassu makudan kudade da kuma karkatar da kudade har naira biliyan 3.5. An gurfanar da a Makanjuola tare da Kolawole, kashiyan majalisan dattijai da Robert Chidozie Mbonu, tsohon manajan kamfanin Societe Generale Bank of Nigeria (SGBN).

Sauran sun hada da Melrose General Service Limited da Obiora Amobi, manajan ayyuka na kamfanin Melrose General Services Limited . Sake gurfanar da su ya biyo bayan canja tsohon alkali, Justis Babs Kuewumi, daga Lagas.

Hukumar EFCC ta sake gurfanar da hadimin Saraki, Makanjuola da sauran su
Hukumar EFCC ta sake gurfanar da hadimin Saraki, Makanjuola da sauran su
Asali: Facebook

A roko da suka gabatar, lauya mai zartarwa, Bashir Kamik, ya bukaci kotun da ta kafa kwanan watan don sauraran karan.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Sanatocin APC da na PDP sun yi musayar yawu akan gudanarwar zabe

Har ila yau dai, lauyan dake kare masu laifin na biyu da na hudu, Okwudili Anozie, yace ya kamata kotun ta baiwa masu laifin damar cigaba da beli da Justis Kwewumi ya bayar.

Har ila yau, lauya ga mai laifi na uku, Omeoga Chukwu, ya bukaci kotun da ta ba abokin huldansa damar cigaba da beli, saboda haka, Justis Maureen Onyetenu ta baiwa rokon mai laifin da ya cigaba akan belin baya da aka bayar sannan kotun ta dage sauraran kara zuwa ranakun 20, 21 da 22 ga watan Mayu, 2019.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel