Da duminsa: APGA ta garzaya kotu kan kin amincewa da sakamakon zaben Zamfara

Da duminsa: APGA ta garzaya kotu kan kin amincewa da sakamakon zaben Zamfara

- Jam'iyyar APGA ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar da na 'yan majalisun dokoki na jihar Zamfara

- Bayan nazarin sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar, jam'iyyar APGA ta yanke shawarar garzayawa kotu

- Jam'iyyar ta ce ba ayi amfani da na'urar tantance masu kad'a kuri'a a garuruwan Bindin, Wonaka, Mada, Kware, Kurya, Dansadau, Cigama da sauransu ba

Jam'iyyar APGA ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar da na 'yan majalisun dokoki na jihar Zamfara. Haka zalika jam'iyyar ta yanke shawarar garzayawa kotun da aka samar domin sauraron korafe korafen zabe.

Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi, dan takarar gwamnan jihar Zamfara karkashin jam'iyyar APGA, ya ce bayan gudanar da tuntuba da kuma sake nazarin sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar, jam'iyyar ta yanke shawarar garzayawa kotu.

A cikin wata sanarwa da shinkafi ya rabawa manema labarai, ya bayyana cewa sakamakon zaben da aka sanar bai yi dai-dai da kuri'un da aka kad'a a jihar ba, yana mai cewa jami'an jam'iyyar a Bindin, Wonaka, Mada, Kware, Kurya, Dansadau, Cigama, da wasu yankuna na Zamfara sun bayyana cewa ba a yi amfani da na'urar tantance masu kad'a kuri'a a kusan kananan hukumomi 13 na jihar ba.

KARANTA WANNAN: Zama bai kare ba: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun yi watsi da tazarcen Buhari

Da duminsa: APGA ta garzaya kotu kan kin amincewa da sakamakon zaben Zamfara
Da duminsa: APGA ta garzaya kotu kan kin amincewa da sakamakon zaben Zamfara
Asali: UGC

"Jami'an tsaro, jami'an INEC da kuma kungiyar sa kai na gwamnati da aka fi saninsu da 'YANSAKAI' sun yi hadaka wajen murde zaben jihar tare da tauye hakkin jama'ar jihar Zamfara da suka zabi jam'iyyarmu ta APGA."

Ya ce: "Kasancewar sakamakon zaben bai haska kuri'un da aka kada a jihar ba, wannnan ya sa muka yanke shawarar garzayawa kotu domin nuna kin amincewa da sakamakon. Haka zalika zamu kalubalanci yadda aka bari APC ta gabatar da 'yan takarar bayan an san cewa ba su gudanar da zaben fitar da gwani ba."

Dan takarar gwamnan na APGA ya ce sun kuma gano yadda aka murde sakamakon zaben kananan hukumomi 8 inda aka tabbatar jam'iyyar APGA ce ta samu nasara da tazara mai yawa, amma aka bayyana APC a matsayin wacce ta lashe zaben kananan hukumomin.

"Muna Allah-wadai da yadda aka yi amfani da jami'an tsaro a wasu sassa na jihar a yayin zaben. Karamin misali shi ne yadda aka yi amfani da sojoji, 'yan sandan sintiri da kuma YANSAKAI a Talata Mafara, Shinkafi, Gusau, Maru, Maradun, Tsafe, Kaura Namoda."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel