An kama mutane uku na sayan katin zabe a Kano

An kama mutane uku na sayan katin zabe a Kano

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce jami'anta sun damke wasu mutane uku da ake zargi da sayan katin zabe daga hannun mutane domin yin magudi a zaben gwamna da za a maimaita a wasu sassan jihar.

Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna ne ya bayar da wannan sanarwar a jiya inda ya ce wadanda aka kama sun hada da Sa'adatu Isma'il mai shekaru 39 da ke zaune a Brigade Quaters da Halima Abba mai shekaru 55 da ke zaune a Tal'udu Quaters.

Ya ce an kama su ne a ranar Talata misalin karfe 8 na dare bayan samun bayanan sirri na cewar suna sayen katin zaben mutane a Gama Quaters da ke karamar hukumar Nasarawa na jihar Kano.

DUBA WANNAN: Za ayi bala'i idan ku ka yi yunkurin magudi a zabukan da za a maimaita - Gargadin 'yan majalisa ga INEC da APC

An kama mutane uku na sayan katin zabe a Kano
An kama mutane uku na sayan katin zabe a Kano
Asali: Twitter

"Wadanda ake zargin suna sayan katin ne a kan kudi N5,000 sannan an same su da kati guda takwas da kudi N10,000," inji Haruna.

Ya kuma ce a ranar 13 ga watan Maris an kama wani Mukhtar Shu'aibu mazaunin Dandishe Quaters a Kano misalin karfe 10 na safe inda shima ya ke sayan kuri'un al'umma a yankin.

Ya kara da cewa da kyar aka ceto rayuwarsa daga hannun wasu mafusatan matasa da ke neman su kashe shi.

Ya yi kira ga al'ummar jihar su fahimci cewa sayar da kuri'a laifi ne da aka tanadarwa hukunci a karkashin dokar Zabe na kasa.

Muna kira ga al'umma suyi gaggawar sanar da hukuma idan sun ga wani na sayan kuri'u domin a kama shi, a gudanar da bincike kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel