Hana ni shedar lashe zabe kan iya hadasa fitina a Imo - Okorocha

Hana ni shedar lashe zabe kan iya hadasa fitina a Imo - Okorocha

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya ce rashin bashi takardan shedan lashe zabe da hukumar zabe mai zaman kanta INEC tayi kan iya tayar da rikici a jihar Imo.

A yayin da ya ke tsokaci a kan lamarin, Okorocha ya ce matakin da INEC ta dauka na rike masa takardan shedan zabe zabe a kan zargi ba tare da jin ta bakinsa ba rashin adalci ne.

A baya dai INEC ta fitar da sunayen 'yan takarar da suka lashe zabe da za a bawa takardan shedan lashe zaben.

DUBA WANNAN: Za ayi bala'i idan ku ka yi yunkurin magudi a zabukan da za a maimaita - Gargadin 'yan majalisa ga INEC da APC

Hana shedar lashe zabe kan iya hadasa fitina a Imo - Okorocha
Hana shedar lashe zabe kan iya hadasa fitina a Imo - Okorocha
Asali: UGC

A cikin jerin sunayen sanatoci, akwai kujeru 109 sai dai an cire sunan Okorocha daga jerin sunayen saboda ikirarin da baturen zabe na jihar, Farfesa Innocent Ibeabuchi ya yi na cewa an tilasta shi ne fadan sakamakon mazabar da sakamakon zaben.

Sai dai a ba bangarensa, Okorocha ya ce matakin da INEC ta dauka cin zarafi ne kuma izgili ne ga demokradiyar Najeriya.

A yayin da ya ke yiwa wasu matasa jawabi a gidan gwamnati da ke Owerri babban birnin jihar Imo, Okorocha ya yi ikirarin cewa ya san INEC ta hada kai da wasu makiyansa domin hana shi nasarar da ya samu.

Ya yi kira ga hukumar ta INEC ta daure ta dauki matakin da ya da ce ta tabbatar masa da nasararsa ta kuma mika masa takardan shedan lashe zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel