Zama bai kare ba: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun yi watsi da tazarcen Buhari

Zama bai kare ba: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun yi watsi da tazarcen Buhari

Yan Nigeria mazauna kasashen waje, karkashin kungiyar GCSDN, ta ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da aka kammala a ranar 23 ga watan Fabreru, inda aka bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben, kungiyar tana mai cewa an tafka magudi a zaben.

Da ya ke jawabi a madadin kungiyar, kodinetanta na fadin duniya, Frederick Odorige, wanda ya yi jawabi daga Budapest, Hungary, ya bayyana zaben a matsayin wanda ke cike da kura kurai, wanda ba a taba samun zabe mai muni irinsa ba tun da aka haifesa sai wannan karon.

"Zaben na cike da kashe kashe, tafka magudi, satar akwatin zabe da kuma lalata takardun kad'a kuri'a wanda yan bangar siyasa aka dauki hayarsu suka aikata. Jami'an soji masu ladabi ga Muhammadu Buhari sun ci karen su ba babbaka a wajen zaben," cewar Odorige.

KARANTA WANNAN: A yau INEC za ta rabawa sanatoci 102 da 'yan majalisu 338 takardun shaidar cin zabe

Zama bai kare ba: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun yi wasti da tazarcen Buhari
Zama bai kare ba: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun yi wasti da tazarcen Buhari
Asali: Depositphotos

A cewar sa, "Zaben da aka kashe fararen hulda da basu ji ba basu gani ba har 47, ba zai taba zama zabe ba."

Akan hakan, kungiyar ta yi nuni da cewa babu wani rikici da aka bayyana cewa sabbin 'yan takarar shugaban kasar ne suka haddasa daga sabbin jam'iyyu.

Kungiyar ta koka kan cewar matasan Nigeria sun mayar da kansu marasa amfani inda suke barin 'yan siyasa marasa kishin kasa ke amfani da su a matsayin yan bangar siyasa mai makon hada kai da matasan 'yan takarar shugaban kasa wajen ganin an cimma mafarkin Nigeria na samun matashin shugaban kasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel