Wani dan kashenin Buhari ya fara tattaki daga Abuja zuwa Kebbi

Wani dan kashenin Buhari ya fara tattaki daga Abuja zuwa Kebbi

Wani dan kashenin sshugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara tattaki daga babbar birnin tarayya Abuja zuwa Kebbi a ranar LKaraba, 13 ga watan Maris.

Ahmed Sani, wani mamba a kungiyar magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma Shugaban kwamitin goyon bayan Shugaban kasa, ya dade da fara tattaki daga yankin Zuba na Abuja a ranar Laraba da misalilin karfe 5:00 na asuba.

Ana sanya ran cewa zai tsaya a gidajen gwamnati da ke Minna, Birnin Kebbi da kuma Sokoto domin mika wasikun biiyayya ga gwamnoni da sanatoci a jihohin uku akan nasarar da APC ta samu a zaben Shugaban kasa, na gwamnoni da kuma zaben sanatoci.

Wani dan kashenin Buhari ya fara tattaki daga Abuja zuwa Kebbi
Wani dan kashenin Buhari ya fara tattaki daga Abuja zuwa Kebbi
Asali: Facebook

Yayinda yake zantawa da manema labarai jim kadan kafin fara tattakin nasa yace: “Zan fara tattakin da karfe 5:00 na asuba daidai. Ina burin sanar da kwamitin goyon bayan shugaba Buhari na jihar Kebbi da dukkanin shugabannin kungiyar cewa yanzun nan zan bar Zuba, Abuja kan hanyana na zuwa Kebbi.”

KU KARANTA KUMA: A yau INEC za ta rabawa sanatoci 102 da 'yan majalisu 338 takardun shaidar cin zabe

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta na ganin ta gyara sannan ta dawo da tarin asarar da kasar ta fuskanta, “sannan kuma za a ga alfanu sosai tattare da kokarinmu.”

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar jakadai, wadanda suka zo fadar Shugaban kasa Abuja domin yi masa murnar samun tazarce.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel