A yau INEC za ta rabawa sanatoci 102 da 'yan majalisu 338 takardun shaidar cin zabe

A yau INEC za ta rabawa sanatoci 102 da 'yan majalisu 338 takardun shaidar cin zabe

- A yau Alhamis 14 ga watan Maris ake sa ran INEC za ta raba takardun shaidar cin zabe ga mambobin majalisar tarayya, a dakin taro na kasa (ICC) da ke Abuja

- Idan aka yi bitar 'yan majalisun tarayyar da suka samu nasara, jam'iyyar APC na da sanatoci 63, jam'iyyar PDP na da 38 ya yin da jam'iyyar YFP ke da kujera daya

- A bangaren majalisar wakilan tarayya kuwa, jam'iyya mai mulki tana da mafi rinjaye da kujeru 211, yayin da PDP ke da kujeru 111

A yau Alhamis 14 ga watan Maris ake sa ran hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC za ta raba takardun shaidar cin zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabreru ga mambobin majalisar tarayya, a dakin taro na kasa (ICC) da ke Abuja.

A cewar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, sanatoci 102 ne za su samu takardun shaidar cin zabensu da misalin karfe 10 na safiya, yayin da 'yan majalisun wakilan tarayya 338 za su samu takardunsu da misalin karfe 2 na rana.

Idan aka yi bitar 'yan majalisun tarayyar da suka samu nasara, jam'iyyar APC na da sanatoci 63, jam'iyyar PDP na da 38 ya yin da jam'iyyar YFP ke da kujera daya.

KARANTA WANNAN:

A yau INEC za ta rabawa sanatoci 102 da 'yan majalisu 338 takardun shaidar cin zabe
A yau INEC za ta rabawa sanatoci 102 da 'yan majalisu 338 takardun shaidar cin zabe
Asali: UGC

An bayyana zaben kujeru 7 a matsayin zaben da bai kammala ba, inda kuma za a sake gudanar da zaben kujerun a ranar 23 ga watan Maris.

A bangaren majalisar wakilan tarayya kuwa, jam'iyya mai mulki tana da mafi rinjaye da kujeru 211, yayin da PDP ke da kujeru 111.

Sauran jam'iyyun siyasar da suka raba sauran kujerun 16 sun hada da jam'iyyar APGA (6), ADC (3), AA (2) da kuma PRP (2). Jam'iyyar ADP, APM da SDP na da kujera daya kowacce.

Har yanzu dai akwai kujeru 22 da ba a cike ba kasancewar ba a kammala zabensu ba. An shirya gudanar da zabensu a karo na biyu a fadin kasar (in banda jihar Rivers) a ranar 23 ga watan Maris.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel