A yau INEC zata gabatarwa sabbin yan majalisa takardar shaidar nasarar zabe, amma banda mutum 1

A yau INEC zata gabatarwa sabbin yan majalisa takardar shaidar nasarar zabe, amma banda mutum 1

A ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC zata gabatarwa dukkan yan takarar majalisan da sukayi nasara a zaben ranar 23 ga watan Febrairu takardar shaidar nasara.

Game da cewar hukumar, za'a gudanar da taron mika takardar shaidan ne a dakin taron farfajiyar ICC dake Area 8, birnin tarayya Abuja.

Ga sabbin sanatoci, za'a gabatar musu da takardar tasu misalin karfe 10 da safe amma yan majalisar wakilai sai karfe 2 na rana.

Gabanin yau, mun kawo muku jerin sunayen sabbin yan majalisan da sukayi nasara a zaben watan Febrairu.

KU KARANTA: Jerin sunayen sabbin yan majalisan wakilan Najeriya 360

A jerin, akwai kujerar yan majalisar dattawa 109 amma har yanzu ba'a kammala zaben wadansu ba kuma wasu an soke sunayensu.

Babban wanda aka sakoe sunansa shine gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, wanda ya lashe zabe domin wakiltar Imo ta yamma.

Game da cewar INEC, an soke sunansa ne saboda zargin cewa wakilansa sun tilasta baturen zaben sanar da shi matsayin zakaran zaben.

Amma gwamnan ya karyata hakan kuma ya bayyana cewa INEC ba tada ikon hanashi takarar shaidarsa.

A jawabinsa, shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ba zata lamunci halayen banza ba kuma saboda haka, ba zata bashi takardar shaidar nasara ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel