Maganar gaskiya: Ba mu kashe ko daya daga cikin wadanda ake zargi a Ondo ba - NSCDC

Maganar gaskiya: Ba mu kashe ko daya daga cikin wadanda ake zargi a Ondo ba - NSCDC

- Rundunar NSCDC ta karyata jita jitar da ake yadawa na cewar ta kashe wani da ake zargi mai suna Rasak Ahmed, da ke tsare a hannunta

- Rahotanni sun bayyana cewa an cafke mamacin ne biyo bayan kama ci da laifin saduwa da diyarsa mai shekaru 8 ta dubura a Akure, babban birnin jihar

- Rundunar ta kara da cewa NSCDC ta farin hula ce kuma ba ta tsananta horo ga masu laifi balle har ta kai ga kisa

Rundunar tsaro ta Civil Defence Corps (NSCDC), reshen jihar Ondo, ta karyata jita jitar da ake yadawa na cewar ta kashe wani da ake zargi mai suna Rasak Ahmed, da ke tsare a hannunta.

Rahotanni sun bayyana cewa an cafke mamacin ne biyo bayan kama ci da laifin saduwa da diyarsa mai shekaru 8 ta dubura a Akure, babban birnin jihar.

Jami'in watsa labarai na hukumar NSCDC, Samuel Oladapo, ya ce rundunar ta yanke hukuncin mayar da martani kan rahotannin da ake yadawar a wasu jaridun kasar na cewa rundunar ta yiwa Ahmed dukan kawo wuka wanda har ta kai ga mutuwarsa.

Oladapo ya ce wanda ake zargin an cafke shi a ranar Lahadi biyo bayan wani korafi da yaronsa, Ibrahim ya shigar na cewar mahaifin nasa na saduwa da kanwarsa.

KARANTA WANNAN: Ba zamu ragawa PDP ba - APC ta sha alwashin samun nasara a zabukan da za a sake

Maganar gaskiya: Ba mu kashe ko daya daga cikin wadanda ake zargi a Ondo ba - NSCDC
Maganar gaskiya: Ba mu kashe ko daya daga cikin wadanda ake zargi a Ondo ba - NSCDC
Asali: Depositphotos

Ya ce: "A yayin da muke gudanar da bincike, Ahmed ya amince da aikata laifin da ake zarginsa yana mai alakanta hakan da aikin shaidan.

"Kafin ma mu rufe shi a cikin dakin rufe masu laifi, ya roki rundunar da ta barshi ya sanya kayansa na 'buba' da 'sokoto' saboda yana jin sanyi, wanda kuma muka amince da hakan.

"Sai dai, a lokacin da aka kawo shi shelkwatarmu da misalin karfe 6 na yamma, cikin mamaki, a lokacin da jami'inmu ya je kai masa abinci, muka tarar da shi ya rataye kansa a jikin karfen kofar dakin kasancewar gajere."

Ya kara da cewa rundunar NSCDC ta farin hula ce kuma ba ta tsananta horo ga masu laifi balle har ta kai ga kisa. Haka zalika ya bayyana cewa tuni aka garzaya da gawar zuwa babban asibitin gwamnati dake jihar, inda rundunar 'yan sanda suka fara bincike bayan tabbatar da mutuwarsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel