Akwai yiwuwar mu kalubalanci nasarar PDP a Oyo – inji Shugaban APC

Akwai yiwuwar mu kalubalanci nasarar PDP a Oyo – inji Shugaban APC

- Jam’iyyar APC tace za ta duba lamarin zaben Gwamna da aka yi a Oyo

- APC mai mulki a Najeriya tace babu mamaki ta shiga Kotu ta kai kara

- Jam’iyyar PDP ta karbe mulkin Jihar daga hannun APC a zaben na bana

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta fara tunanin yiwuwar zuwa kotu bayan ta sha kashi a zaben gwamna a jihar Oyo. Shugaban jam’iyyar APC a jihar ta Oyo, Cif Akin Oke, ya bayyanawa ‘yan jarida wannan a jiya Laraba.

A wata hira da shugaban APC na Oyo gaba daya yayi da manema labarai, ya bayyana cewa jam’iyyar ta su, tana duban yanayin zaben gwamna da ‘yan majalisun dokoki na jihar da aka yi da idanun basira bayan sun sha kashi.

KU KARANTA: Wani Malami a Najeriya ya fadawa 'Dan takarar PDP cewa zai yi mulki

Akwai yiwuwar mu kalubalanci nasarar PDP a Oyo – inji Shugaban APC
Oluseyi Makinde na PDP ya doke Adebayo Adelabu a jihar Oyo
Asali: UGC

Akin Oke ya nuna cewa lallai akwai yiwuwar jam’iyyar APC ta shiga kotu ta kai kara bayan ta rasa mulkin jihar Oyo a hannun PDP. Yanzu haka Lauyoyin jam’iyyar ta APC za su yi nazari sannan su dauki duk matakin da ya dace.

Shugaban APC na Oyo, ya kuma godewa dubban ‘ya ‘yan jam’iyyar da Magoya bayan su da su ke mara masa baya da su kwantar da hankalin su, kana su cigaba da bada hadin-kai. Jam’iyyar tace za tayi abin da ya dace game da zaben.

Jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben gwamnan jihar da aka yi inda ‘dan takarara hamayya watau Seyi Makinde ya samu nasara. Adebayo Adelabu wanda ya nemi ya gaji Abiola Ajimobi ya sha kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel