Kan zaben gwamna, Babban hadimin Ganduje ya ajiye aikinsa

Kan zaben gwamna, Babban hadimin Ganduje ya ajiye aikinsa

Alhaji Hashim Suleiman, babban hadimin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kan kawata birane, ya yi murabus daga kujerarsa bisa ga kin runguman kaddara da gwamnan yayi kan sakamakon zaben ranar Asabar.

Hashim Suleiman ya gabatar da takardar murabus dinsa ne ga sakataren gwamnatin jihar ranar Laraba, 14 ga watan Maris, 2019.

A wasikar da ya aika, ya godewa gwamnan da damar da ya bashi na bautawa jihar yayinda ya bayyana cewa dalilin murabus dinsa shine rashin rungumar kaddara da Ganduje ya gaza yi bayan ya bayyana cewa dan takarar jam'iyyar People’s Democratic Party, PDP, Abba Kabir Yusuf, ya lashe zabe.

Ya kara cewa Abba Gida Gida ya lashe zaben amma hukumar gudanar da zabe ta kasa wato INEC ta ki kammala zaben da wasu boye-boye.

Game da cewarsa, Ganduje a matsayinsa na Khadimul-Islam, ya kamata ya hakura saboda hakan ya zama darasi ga wasu Musulmai masu bautan Allah da iklasi.

A wasikar mai ranar wata, Laraba, 13 ga watan Maris, 2019, wacce ya rattaba hannu da knasa, Suleiman Hashim yace:

"Ina rubuta wannan ne domin sanar da kai kan ajiye aikin a matsayin babban hadiminka kan kawata birane. Ina godiya da damar da bani domin bauta karkashin gwamnatinka."

Asali: Legit.ng

Online view pixel