Tsohon DG, Akingbola, ya rika wawurar kudin mutane yana ba Kamfanonin sa - EFCC

Tsohon DG, Akingbola, ya rika wawurar kudin mutane yana ba Kamfanonin sa - EFCC

Mun ji cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa a Najeriya, ta sake komawa kan zargin Dr Erastus Akingbola na tsohon bankin nan na Intercontinental Bank Plc.

A makon nan ne, hukumar EFCC ta sake komawa gaban babban kotun tarayya da ke Legas da Erastus Akingbola, wanda ya rike babban Darekta a bankin Intercontinental Bank Plc a lokacin bankin yana da rai a Najeriya.

Alkali Mojisola Olatoregun ya sake bude kara mai lamba ta FHC/L/CS/443c/09 a Ranar Litinin dinnan inda ake zargin tsohon Darekta (watau MD) Intercontinental Bank da wawurar kudin bankin ba tare da bin doka ba.

Hukumar EFCC tana zargin tsohon DG din ya bada wani haramtaccen bashi na Naira Biliyan 8 ga wasu kamfanoni da su ka hada da Soo-Kok Holding Limited, Tofa General Enterprises, Cinca Nigeria Limited a 2007 zuwa 2009.

KU KARANTA: Alkalai sun ba Femi Fani-Kayode da Yinka Odumakin gaskiya a Kotu

Tsohon DG, Akingbola, ya rika wawurar kudin mutane yana ba Kamfanonin sa - EFCC
Ana zargin Akingbola da ba kamfanonin sa bashi daga kudin mutane
Asali: Depositphotos

Babban Darektan wannan banki wanda yanzu ya ruguje, ya sa hannu wajen daukar makudan kudi har Naira Biliyan 8 ga kowane daga cikin wadannan kamfanoni ba tare da sun cika sharudan karbar bashi ba inji hukumar ta EFCC.

Daga cikin ragowar kamfanonin da aka ba wannan mahaukatan bashi akwai kamfanin Harmony Trust and Investment Limited, da kuma wani kamfani mai suna Stanzus Investment Limited. Yanzu dai an daga karar zuwa makon gobe.

Tsohon babban Darektan bankin dai ya bayyanawa kotu cewa bai aikata laifin da ake tuhumar sa da shi ba. Abdulraheem Jimoh da Rotimi Jacobs su ne Lauyoyin da su kai kara gaban Alkali mai shari’a Mojisola Olatoregun a Legas.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel