Albashir ya kafa sabuwar gwamnati don tausan jama’an kasar Sudan

Albashir ya kafa sabuwar gwamnati don tausan jama’an kasar Sudan

Shugaban kasar Sudan, Omar Albashir ya sanar da rusa gwamnatin kasar gaba daya, tare da nadin sababbin ministoci da zasu tafiyar da gwamnatin kasar don tausan al’ummar kasar da suka kwashe tsawon lokaci suna gudanar da zanga zanga.’

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Laraba, 13 ga watan Maris ne Albashir ya sanar da kafa sabuwar gwamnatin nasa, bayan sanar da dokar ta baci, tare da rusa gwamnatin tarayyar kasar da ma gwamnatocin jahohi.

KU KARANTA: Koda tsiya tsiya sai mun ci zaben nan – shugaban APC ta Kano

Albashir ya kafa sabuwar gwamnati don tausan jama’an kasar Sudan
Albashir
Asali: UGC

Dama tun a baya ne shugaban ya dauki alwashin kafa sabuwar gwamnati data kunshi kwararru wadanda suka goge a fannoni daban daban, kuma suka nuna kwarewa da sanin makaman aiki domin su shawo kan matsalar halin rushewar tattalin arziki da kasar ta shiga.’

Daga karshe dai an jiyo Firai Ministan kasar, Mohammed Taher Eila ya sanar da cika wannan alkawari, inda yace “Ina sanar da kafa sabuwar gwamnati a kasar Sudan data kunshi manistocin tarayya guda 21, da kananan ministoci 18 da zasu magance matsalar tattalin arzikin kasar.”

Wannan matsalar rushewar tattalin arzikin kasar Sudan tayi sanadiyyar mutuwar al’ummar kasar da dama, musamman masu zanga zanga da Yansanda suka bindigesu yayin da suka gudanar da zanga zangar kin jinin gwamnati, tare da bukatar Albashir ya sauka daga mulki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel