Yansanda sun yi ram da wani dan majalisa dake da hannu cikin kisan wani dan majalisa

Yansanda sun yi ram da wani dan majalisa dake da hannu cikin kisan wani dan majalisa

Rundunar Yansandan jahar Oyo ta cafke bulaliyar majalisar dokokin jahar Oyo, Wasiu Olasifoye Akinyomeyede bisa zarginsa da hannu cikin kisan dan takarar Sanatan jam’iyyar ADP, Temitope Olatoye Sugar, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Asabar data gabata ne yan bindiga suka bindige Olatoye wanda dan majalisar wakilai ne dake wakiltar mazabar Akinyele/ Lagelu, kuma ya tsaya takarar Sanata a zaben da aka gudanar makonni uku da suka gabata, amma ya fadi.

KU KARANTA: Koda tsiya tsiya sai mun ci zaben nan – shugaban APC ta Kano

Rahotanni sun bayyana cewa akwai tsatstsamar dangantaka tsakanin dan majalisa Olatoye da dan majalisa Olasifoye wanda ke wakiltar mazabar Legelu a majalisar dokokin jahar Oyo, sakamakon dukkanin sun fito ne daga yanki daya.

A daren Talata Yansanda suka kama Wasiu Olasifoye, inda suka yi awon gaba dashi zuwa babban ofishinsu dake babban birnin tarayya Abuja, kuma tuni rundunar ta sanar da kaakakin majalisar dokokin jahar Oyo, Olagunju Ojo.

Sai dai Kaakaki Olagunju ya bayyana cewa “Bani da masaniyar sun wuce dashi babban birnin tarayya Abuja, abinda na sani kawai shine Yansanda sun kamashi, kuma suna bincikensa, amma ban san inda suka kaishi ba.”

A wani labarin kuma, An jiyo shugaban APC reshen jahar Kano, Abdullahi Abbas yana bayyana zaben maimaicin da za’a gudanar a jahar Kano a matsayin na ‘A mutu ko ayi ra’ a cikin wani faifan bidiyo, inda yace koda tsiya tsiya sai sun ci zaben.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel