Sowore yayi kaca-kaca da Minista bayan yace babu jirgin a Boeing 737-MAX-800 Najeriya

Sowore yayi kaca-kaca da Minista bayan yace babu jirgin a Boeing 737-MAX-800 Najeriya

- Kwanan nan ne wani jirgin 737-MAX-800 ya kife a kasar waje

- Ministan jirage yace babu irin wannan jirgi ko guda a Najeriya

- Sowore yace hakan ya nuna ci-baya ne ba wai hangen nesa ba

Fitaccen ‘dan fafutukar nan, kuma wanda ya nemi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar AAC a zaben da aka yi kwanan nan watau Omoyele Sowore ya caccaki Ministan harkokin jirgin saman Najeriya a Facebook.

Omoyele Sowore yayi magana game da hadarin jirgin saman Boeing 737-MAX-800 na kamfanin jiragen kasar Habasha watau Ethiopian Airlines, da ya auku a karshen makon jiya, inda duka fasinjojin ciki har 157 su ka mutu.

KU KARANTA: Ajali ya kira Malamin Najeriya da yayi fice a Duniya a hadarin jirgi

Sowore yayi kaca-kaca da Minista bayan yace babu jirgin a Boeing 737-MAX-800 Najeriya
Sowore ya soki Minista bayan yace babu jirgin Boeing 737-MAX-800 a Najeriya
Asali: Depositphotos

Wannan mummunan hadari da ya auku ne ya sa manyan kasashen Duniya irin su kasar Australliya Birtaniya, da China da sauran su, su ka dauki mataki na hana jirgin tashi. An yi hakan ne dai saboda kare rayukan al’ummar su.

Shi kuwa Ministan na Najeriya, Hadi Sirika, ya fito yayi bayani inda yace ka da hankalin mutanen kasar ya tashi game da wannan hadari, inda ya tabbatar da cewa sam babu kirar jirgin Boeing 737-MAX-800 a kaf sararin Najeriya.

‘Dan takarar shugaban kasar yace wannan ba abin burgewa bane, illa iyaka ya nuna rashin cigaban Najeriya. Sowore yace rashin bunkasar mu ce ta sa babu wannan jirgi, ba wai wani hangen nesa bane Ministan yayi a kan batun.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel