Taraba: Jami'an DSS sun gano katunan zabe 350 a gidan hadimin gwamna Darius

Taraba: Jami'an DSS sun gano katunan zabe 350 a gidan hadimin gwamna Darius

- Hukumar tsaro ta DSS a jihar Taraba ta samu nasarar cafke akalla mutane ukku da ta kamasu da katunan zabe sama da 300

- Katunan zaben, a cewar DSS, an same su ne a gidan wani hadimi na musamman ga gwamnan jihar Darius Ishaku, wanda aka biye sunansa

- Hukumar ta cafke wadanda ake zargin ne biyo bayan wani rahoto da rundunar 'yan sanda ta samu tare da hadin guiwar wasu hukumomin tsaro

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu na nuni da cewa hukumar tsaro ta DSS a jihar Taraba ta samu nasarar cafke akalla mutane ukku da ta kamasu da katunan zabe sama da 300. Haka zalika hukumar ta gabatar da wadanda ake zargin gaban manema labarai.

Mukaddashin daraktan hukumar DSS na jihar, Tunji Bakari, ya gabatar da wadanda ake zargin a garin Jalingo, babban birnin jihar.

Ya ce hukumar ta samu nasarar cafke wadanda ake zargin ne biyo bayan wani kwakkwaran rahoto da rundunar 'yan sanda ta samu tare da hadin guiwar wasu hukumomin tsaro.

KARANTA WANNAN: Ba zamu ragawa PDP ba - APC ta sha alwashin samun nasara a zabukan da za a sake

Taraba: Jami'an DSS sun gano katunan zabe 350 a gidan hadimin gwamna Darius
Taraba: Jami'an DSS sun gano katunan zabe 350 a gidan hadimin gwamna Darius
Asali: UGC

Katunan zaben, a cewar DSS, an same su ne a gidan wani hadimi na musamman ga gwamnan jihar Darius Ishaku, wanda aka biye sunansa.

Sauran kayayyakin da aka samu a gidan hadimin gwamnan da ke yankin Mayo-gwai a Jalingo sun hada da adduna, kwari da baka da kuma sauran makamai da ake hadawa a cikin gida.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel