Babu shakka zamu gudanar da zaben gaskiya da gaskiya a jahar Kano – INEC

Babu shakka zamu gudanar da zaben gaskiya da gaskiya a jahar Kano – INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta bada tabbacin shirya zaben gaskiya da adalci a zaben maimaici da zata gudanar a jahar Kano a ranar 23 ga watan Maris, kamar yadda shugaban hukumar reshen jahar Kano, Farfesa Riskuwa Arabu Shehu ya bayyana.

A wannan zabe dake karatowa ne za’a samu sahihi kuma halastaccen dan takarar daya lashe zaben gwamnan jahar Kano, biyo bayan sanar da rashin kammaluwar zaben da INEC tayi saboda lalatattun kuri’un da aka kada sun haura bambancin kuri’un dake tsakanin Ganduje da Abba na PDP.

KU KARANTA: Mijina ya kashe diyarmu don yin tsafin samun kudi – Uwargida ga Kotu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Riskuwa na fadin hukumar ta dauki wannan mataki ne sakamakon rikice rikicen da aka samu a wasu akwatuna, da kuma matsalar aringizon kuri’u, wanda hakan yasa aka soke zaben a wasu rumfuna 210 cikin kananan hukumomi 22.

“Ina sanar da jama’a cewa a ranar Asabar, 23 ga watan Maris ne zamu gudanar da wannan zabe, kuma zamu tabbatar ya gudana cikin gaskiya da adalci. Zaben ya shafi rumfunan zabe 210, a mazabu 88 dake da kuri’u 128,572.” Inji shi.

A zaben makon daya gabata, dan takarar jam’iyyar PDP, Abba gida gida ya samu kuri’u 1,014,474, yayin da dan takarar jam’iyyar APC, Gwamna Abdullahi Ganduje ya samu 987,819, bambancin kuri’u 26,655, wanda bai kai adadin lalatattun kuri’u 128,572 ba.

A wani labarin kuma, An jiyo shugaban APC reshen jahar Kano, Abdullahi Abbas yana bayyana zaben maimaicin da za’a gudanar a jahar Kano a matsayin na ‘A mutu ko ayi ra’ a cikin wani faifan bidiyo, inda yace koda tsiya tsiya sai sun ci zaben.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel