Koda tsiya tsiya sai mun ci zaben nan – shugaban APC ta Kano

Koda tsiya tsiya sai mun ci zaben nan – shugaban APC ta Kano

Wani faifan bidiyo da a yanzu haka ya mamaye shafukan sadarwar yana gizo ya bayyana yadda shugaban jam’iyyar APC reshen jahar Kano, Abdullahi Abbas ya bayyana zaben maimaici da hukumar INEC zata shirya don kammala zaben gwamnan jahar dole a matsayin ‘A mutu ko ayi rai’.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Abdullahi yana bayyana ma magoya bayan jam’iyyar APC cewa zasu basu cikakken tsaro a yayin zabukan, koda kuwa hakan na nufin sallamar duk wasu jami’an Yansanda da zasu kwantar da tarzoma, daga aiki.

KU KARANTA: Mijina ya kashe diyarmu don yin tsafin samun kudi – Uwargida ga Kotu

Abdullahi ya bayyana wadannan kalamai ne a yayin da wasu ayarin matasa suka kai masa ziyara a gidansa, inda ya shawarcesu dasu kawar da duk wani abokin hamayya daya shige musu gaba a ranar zabe.

Ga bidiyon nan kamar yadda ma'abocin shafin Facebook, Abbas Abdurrashid ya daura.

“Akwai yiwuwar za’a iya kamaku a ranar zabe, amma ina tabbatar muku kafin ku isa ofishin Yansanda zamu kwatoku, kum duk dansandan daya kamaku sai ya bar aiki. Zamu baku duk irin kariyar da kuke bukata, zaben nan a mutu ko ayi rai ne a wajenmu, koda tsiya tsiya sai mun ci shi.” Inji shi.

Idan za’a tuna hukumar INEC ta sanar da rashin kammaluwar zaben gwamnoni a jahohi shida da suka hada da Kano, Benuwe, Sakkwato, Adamawa, Bauchi da Filato, sakamakon lalatattun kuri’un da aka kada a zaben sun fi yawa fiye da bambancin dake tsakanin yan takarar dake kan gaba.

Don haka INEC ta sanya ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranar da zata kammala wannan zabe, kafin sannan a jahar Kano, dan takarar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ne ke kan gaba, yayin da gwamnan jahar, Abdullahi Umar Ganduje ke bi masa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel