Don girman Allah, kar ka biyewa Bindow a murde zaben Adamawa – PDP ta roki Buhari

Don girman Allah, kar ka biyewa Bindow a murde zaben Adamawa – PDP ta roki Buhari

Jam’iyyar PDP a jihar Adamawa, tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa ka da ya tsoma hannun sa a cikin zaben sabon gwamnan jihar ta Adamawa da har yanzu ba a kammala ba.

Babbar Jam’iyyar hamayyar ta roki shugaban kasar da ya guji jefa kan sa cikin rikicin da gwamna Muhammadu Jibrilla Bindow yake nema ya cusa sa domin ganin an murde zaben yadda jam’iyyar APC za ta dawo tayi nasara.

Shugaban jam’iyyar adawa na jihar, Barista Tahir Shehu, yayi wannan jawabi a lokacin da ya zanta da manema labarai a cikin Garin Yola a jiya Laraba. Shugaban PDP na jihar yace ana neman a hana INEC karasa zaben jihar.

KU KARANTA: Yadda Gwamnatin Kano ta cire wasu Miliyoyi domin shiriya murde zabe

Don girman Allah, kar ka biyewa Bindow a murde zaben Adamawa – PDP ta roki Buhari
Jam’iyyar adawa tace Buhari tamkar Uba ne don haka kar ya bari a murde zabe
Asali: Facebook

Tahir Shehu ya fadawa ‘yan jarida cewa sun fahimci lallai ana yunkurin amfani da kotu domin a haramtawa hukumar zabe na kasa watau INEC cigaba da karasa zaben gwamnan jihar da za ayi a Ranar 23 ga Watan Maris dinnan.

Shugaban jam’iyyar ta PDP yayi kira ga shugaban kasa cewa a matsayin sa na Uba, bai kamata ya biyewa gwamnan na APC wajen yin abin da bai dace ba. Jam’iyyar ta kuma yi tir da irin makukun bashin da gwamnan ya karbowa jihar.

A zaben da aka yi a karshen makon jiya, sakamakon zaben da aka tattara daga kananan hukumomi 21 sun nuna cewa ‘dan takarar PDP watau Ahmadu Fintiri ne yake kan gaba da kuri’a fiye da 32, 476, amma yanzu an dage zaben jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel