Ba zamu ragawa PDP ba - APC ta sha alwashin samun nasara a zabukan da za a sake

Ba zamu ragawa PDP ba - APC ta sha alwashin samun nasara a zabukan da za a sake

- Jam'iyyar APC a jihar Filato ta jaddada cewa za ta zage damtse a yayin da za a sake gudanar da zaben gwamnan jihar da aka shirya yi a ranar 23 ga watan Maris

- Rahotanni sun bayyana cewa gwamna Simon Lalong na APC ya samu kuri'u 583,255 yayin da dan takarar PDP, Sanata Jeremiah Useni ya samu kuri'u 538,326

- INEC ta bayyana zaben jihar a matsayin zaben da bai kammala ba saboda tazarar kuri'u 44, 929 da APC ta baiwa PDP ta yi kasa da kuri'u 49,377 da aka soke

Jam'iyyar APC a jihar Filato ta jaddada cewa za ta zage damtse a yayin da za a sake gudanar da zaben gwamnan jihar da aka shirya yi a ranar 23 ga watan Maris, duk da cewa ita ce akan gaban PDP da tazarar kuri'u 44,929.

Rahotanni sun bayyana cewa sakamakon zaben gwamnan jihar kamar yadda jami'in tattara sakamakon zabe na jihar, Farfesa Richard Anade ya sanar, ya bayyana cewa gwamna Simon Bako Lalong na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 583,255 yayin da dan takarar PDP, Sanata Jeremiah Useni ya samu kuri'u 538,326.

Farfesa Anande ya bayyana zaben jihar a matsayin zaben da bai kammala ba la'akari da cewa tazarar kuri'u 44, 929 da APC ta baiwa PDP ta yi kasa da kuri'u 49,377 da aka soke a fadin kananan hukumomi 9.

KARANTA WANNAN: Dalibai su shirya: Za a fara zana jarabawar JAMB 2019 a ranar 11 ga watan Afrelu

Adams Oshiomhole: Shugaban APC na kasa
Adams Oshiomhole: Shugaban APC na kasa
Asali: UGC

Mataimakin Daraktan kwamitin watsa labarai da kafofin sadarwa na zamani na kungiyar yakin zaben APC, Barista Festus Fuanter a ranar Laraba ya ce jam'iyyar ba zata dauki sake zabena a matsayin wasa ba, illa ma ta kara zage damtse.

Barista Fuanter sai yayi kira ga daukacin al'umma da magoya bayan jam'iyyar APC da su kwantar da hankulansu tare da kasancewa masu bin doka, amma ya bukaci al'ummar da ke zaune a yankunan da za a sake gudanar da zabe da su tabbata sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin kad'a kuri'arsu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel