Dalibai su shirya: Za a fara zana jarabawar JAMB 2019 a ranar 11 ga watan Afrelu

Dalibai su shirya: Za a fara zana jarabawar JAMB 2019 a ranar 11 ga watan Afrelu

- Hukumar zana jarabawar JAMB, ta tsaida ranar 11 ga watan Afrelu a matsayin ranar da dalibai za su zana jarabawar 2019 UTME

- A cewar hukumar, za a fara zana jarabawar gwaji (mock) a ranar 1 ga watan Afrelu a fadin kasar, sabanin ranar 24 ga watan Maris da aka rigaya aka sanar

- Sai dai hukumar ta shawarci duk daliban da suka bayyana ra'ayinsu na jana jarabawar (mpock) kuma suka fitar da takardar tabbaci, da karsu damu da sake fitar da wata takardar

Hukumar zana jarabawar samun gurbin karatu a manyan makarantu ta kasa JAMB, ta tsaida ranar 11 ga watan Afrelu a matsayin ranar da dalibai za su zana jarabawar sharar fagen shiga manyan makarantu UTME.

Hukumar ta sanar da hakan a ranar Laraba a cikin wata sanarwa daga shugaban sashenta na watsa labarai da kafofin sadarwa na zamani, Dr Fabian Benjamin.

A cewar Benjamin, za a fara zana jarabawar gwaji (mock) a ranar 1 ga watan Afrelu a fadin kasar, sabanin ranar 24 ga watan Maris da aka rigaya aka sanar.

KARANTA WANNAN: Kotu za ta saurari bukatar EFCC na kwace kadarorin Patience Jonathan a watan Afrelu

Dalibai su shirya: Za a fara zana jarabawar JAMB 2019 a ranar 11 ga watan Afrelu
Dalibai su shirya: Za a fara zana jarabawar JAMB 2019 a ranar 11 ga watan Afrelu
Asali: Depositphotos

Mai magana da yawun hukumar JAMB ya ce an samu canjin ne sakamakon wasu matsaloli da suka sha kan hukumar. Sai dai ya shawarci duk dalibai, wadanda suka bayyana ra'ayinsu na jana jarabawar gwajin a wajen rejista kuma suka fitar da takardar tabbaci, da karsu damu da sake fitar da wata takardar.

"Sai dai, dalibai za su fara fitar da takardarsu ta 2019 UTME daga ranar Talata 2 ga watan Afrelu, kuma ya zama wajibi dukkanin dalibai su tabbata sun fitar da wannan takarda kafin ranar zana jarabawar."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel