Babbar mota ta murkushe mutane 7 har lahira

Babbar mota ta murkushe mutane 7 har lahira

Akalla mutane bakwai sun rasa rayukansu a ranar Laraba inda wata babbar mota mai daukan Kalanzir ta kutsa cikin yan kasuwa a Upper Iweka, Onitsha, jihar Anambara.

Yayinda tabbatar da labarin, kakakin hukumar yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya bayyana cewa motar ta kwacewa direban ne inda ya murkushe mutane 19.

Yace:"Tawagar jami'an yan sandan a Onitsha sun ziyarci wajen kuma sun kai wadanda suka jikkata asibitin Toronta dake Onitsha, inda mutane bakwai;maza shiga da mace daya, suka rasa rayukansu game da cewar likita."

Ya kara da cewa wasu mutane 12 na jinya a asibitin yayinda aka kai gawawwakin wadanda suka mutu dain ajiye gawawwaki domin bincike.

Game da cewar yan sanda, an kaddamar da bincike kan al'amarin kuma an damke direban mai suna, Agari, kuma an kwace motar.

KU KARANTA: Kungiyar Boko Haram (ISWAP) ta barke gida biyu

A bangare guda, Al'ummar jihar Legas sun waye gari cikin wata annoba na rubzawar makaranta darajar farko wato Nozare da firamare a karamar hukumar Lagos Island dake jihar.

Ginin makarantar mai hawa ukku da ke yankin Itafaji, tsibirin Legas ya rubza a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, 2019. Lamarin da ya haddasa tashin hankali da rudani tsakanin al'ummar da ke zaune a kusa da ginin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel