Zaben Kano: An koma siyen kuri'un mutanen dake rumfunan da za'a sake zabe

Zaben Kano: An koma siyen kuri'un mutanen dake rumfunan da za'a sake zabe

'Yan siyasa a jihar Kano kamar yadda muka samu labari yanzu haka sun koma siyen kuri'un masu damar sake yin zabe a rumfunan mazabun da za'a sake yin zaben gwamna a ranar 23 ga watan Maris.

Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa jami'an 'yan sanda a jihar ta Kano ma sun kama wata mata da aka ce 'yar APC ce tana bi gida-gida tana siyen kuri'un mata daga Naira dubu 5 har zuwa ma dubu 10 a wasu lokuttan.

Zaben Kano: An koma siyen kuri'un mutanen dake rumfunan da za'a sake zabe
Zaben Kano: An koma siyen kuri'un mutanen dake rumfunan da za'a sake zabe
Asali: UGC

KU KARANTA: APC ta bayyana yadda zata fitar da shugabannin majalisa

Sai dai shi kuwa ta bangare daya, dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ya shaida wa BBc cewa ba su taba raba kudi ba domin su sayi kuri'un jama'a.

Ya bayyana wannan ne a wata hira da aka yi da shi kai tsaye a shirin yamma na ranar Talata da BBc ke gudanarwa.

Abba ya bayyana cewa a shirye suke da su karbi zaben da za a sake yi a ranar 23 ga watan Maris hannu biyu domin su sun yi "imani da kaddara."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel