Zaben gwamoni: Akwai ayar tambaya a kan gaskiyar Buhari - Dan majalisar Kano

Zaben gwamoni: Akwai ayar tambaya a kan gaskiyar Buhari - Dan majalisar Kano

Dan majalisar wakilai na tarayya daga jihar Kano, Aliyu Madaki ya ce akwai ayar tambaya a kan gaskiyar Shugaba Muhammadu Buhari duba da yadda aka ki kammala zabukkan gwamnoni a wasu jihohi na Najeriya.

Madaki ya ce ya kamata a sake bibiyar gaskiyar shugaban kasar duba da yadda ya yi gum da bakinsa a kan yadda aka gudanar da zabuka a wasu jihohin Najeriya.

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Dala ya fadi hakan ne yayin da ya ke tofa albarkacin bakinsa a kan wata kudiri da wani dan majalisa ya gabatar a ranar Laraba.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta ce zabuka ba su kammala ba a jihohi shida a Najeriya bayan soke sakamakon zabukkan wasu mazabu a jihohin.

DUBA WANNAN: APC 13, PDP 9: Jerin sunayen sabbin gwamnoni da INEC ta sanar sun lashe zabe

Akwai alamar tambaya a kan gaskiyar Buhari - Dan majalisar Kano
Akwai alamar tambaya a kan gaskiyar Buhari - Dan majalisar Kano
Asali: Twitter

Daga bisani hukumar zaben ta zabi ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranara da za a sake maimaita zabukan a jihohin Benue, Sokoto, Plateau, Adamawa, Kano da Bauchi.

A jawabinsa, Madaki na jam'iyyar PDP ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da kawar da kansa dangane da wasu abubuwan da ba saba gani ba da INEC keyi.

"Idan shugaban kasa yana sauran gaskiya, ya kamata a sake bibiyan wannan gaskiyar. Ba zamu amince ba, ba zamu bari ta faru ba. Ba za ta faru ba."

Ya ce duk da cewa ba zaiyi magudin zabe ko ya goyi bayan hakan ba, "babu wanda zai yi mana magudi" a Kano.

"Babu wanda zai zo Kano ya yi tilasta mana. Kano ba Legas bane," inji shi.

A yayin da ya ke jawabinsa, Muhammad Soba daga jihar Kaduna ya ce INEC ba ta da ikon cewa za be bai kammala ba bayan an gama kirga kuri'u.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel