INEC ta nuna jajircewa wajen sake zabe na gaskiya a jihar Kano

INEC ta nuna jajircewa wajen sake zabe na gaskiya a jihar Kano

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta nuna jajircewa wajen sake zabe na gaskiya a jihar Kano

- INEC ta ce tana nan akan bakarta na gudanar da zabe na gaskiya a zaben gwamnan jihar da za a maimaita a ranar 23 ga watan Maris

- Kwamishinan zabe na jihar, Farfesa Riskuwa Arab-Shehu ya bayyana hakan a wani jawabi a ranar Laraba, 13 ga watan Maris a Kano

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tace ta nan kan bakarta na jajircewa wajen gudanar da zabe na gaskiya da amana a zaben gwamna da za a sake gudanarwa a ranar 23 ga watan Maris a jihar Kano.

Kwamishinan zabe na jihar, Farfesa Riskuwa Arab-Shehu ya bayyana hakan a wani jawabi a ranar Laraba, 13 ga watan Maris a Kano.

INEC ta nuna jajircewa wajen sake zabe na gaskiya a jihar Kano
INEC ta nuna jajircewa wajen sake zabe na gaskiya a jihar Kano
Asali: UGC

Arab-Shehu yace zaben da za a sake ne zai tabbatar da wanda ya lashe zaben gwamna, wanda aka kaddamar a matssayin ba kammalalle ba a ranar Litinin.

Ya ci gaba da bayanin cewa sakamakon zaben da aka soke a wasu mazabun an yi hakan ne saboda rikici da kuma zabe da ya kauce wa kima.

A cewarsa mazabun da abun ya shafa na da adadin masu rijista 128, 572, yayinda tazarar da ke tsakanin Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC) ya kasance 26,655 kacal.

KU KARANTA KUMA: Yanzu: Kananan yara sun mutu, wasu sun makale a yayin da gini ya rubza a Legas

Yayi bayanin cewa soke zaben ya yi daidai da sashi na 41 (e) na tsare-tsare da gudanarwar zaben 2019.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel