Cakwakiya: Sanarwar Orji Kalu ya ci zaben sanata a APC kuskure ne – INEC

Cakwakiya: Sanarwar Orji Kalu ya ci zaben sanata a APC kuskure ne – INEC

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta kamala shirin mika shaidar lashe zaben kujerar sanata ga Orji Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia da ya aka bayyana cewar ya samu nasara a zaben kujerar sanata da aka yi a watan jiya duk da rudanin da ke tattare da sakamakon zaben.

Hakan ta fito fili ne bayan INEC ta saki sunayen sanatoci 100 da aka zaba da zata bawa takardar shaidar lashe zabe da safiyar ranar Alhamis, 14 ga watan Maris.

Sai dai a sakamakon zaben kujerar sanatam jihar Abia ta Arewa da INEC ta saki ya nuna cewar Kalu bai lashe zaben ba saboda tazarar da ke tsakaninsa da wanda ya zo na biyu ta gaza yawan kuri’un da aka soke a mazabun yankin.

Kalu ya samu kuri’u 31,201 yayin da Mao Ohuabunwa na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 20,801 sannan aka bayyana cewar an soke kuri’u 38,526 kamar yadda baturen zabe, Charles Anumudu, ya sanar. Adadin Kuri’un da aka soke ya fi banbancin kuri’u 10,400 da ke tsakanin Kalu da Ohuabunwa.

Cakwakiya: Sanarwar Orji Kalu ya ci zaben sanata a APC kuskure ne – INEC
Buhari da Orji Kalu
Asali: Facebook

Festus Okoye, kakakin INEC, ya shaida wa jaridar Premium Time cewar hukumar ba ta san me zata yi a kan wannan matsala ba tunda tuni an sanar da wanda ya yi nasara.

Okoye ya bayyana cewar babu abinda INEC zata iya yi muddin aka sanar da sakamakon zabe, sai dai wanda abin ya shafa ya nufi kotu domin neman hakkin sa.

DUBA WANNAN: Sunaye: Buhari ya nada manyan darektocin hukumar NSIA

Da aka yi ma sa tunin cewar INEC ta dakatar da bawa Rochas takardar shaidar lashe zaben kujerar sanata, sai Okoye ya ce akwai banbanci tsakanin abinda ya faru da Kalu da na Rochas.

Ya ce INEC ta dakatar da bawa Rochas takardar shaidar ne saboda baturen da aka tura ya sanar da sakamakon zaben ne domin tsira da lafiyar sa biyo bayan barazanar da Rochas ya yi ma sa idan bai bayyana ya ci zabe ba.

Amma a bangaren matsalar sakamakon zaben Kalu, baturen zabe bai fadi cewar an turasasa shi sanar da sakamakon zabe ba ko kuma an yiwa rayuwar sa barazana ba. Hasali ma dukkan wakilan ‘yan takarar kujerar sun saka hannu a kan sakamakon zaben”, a cewar Okoye.

Kazalika, baturen zaben kujerar sanata jihar Abia ta Arewa, Joseph Iloh, ya tabbatar da cewar dukkan wakilan ‘yan takara sun saka hannu a kan sakamakon zaben ba tare da wani korafi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel