Buhari yayi jaje ga iyalan wadanda rushewar ginin Lagas ya cika da su

Buhari yayi jaje ga iyalan wadanda rushewar ginin Lagas ya cika da su

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace yayi matukar bakin ciki da rushewar ginin benen wata makaranta a yankin Itafaaji da ke Lagas, wanda ya haddasa mumunan annoba mussamman akan kananan yara.

Shugaba Buhari ya nuna alhininsa ne a wani jawabin labarai wanda Femi Adesina, kakakin Shugaban kasar ya saki a Abuja a ranar Laraba, 13 ga watan Maris.

Legit.ng ta tattaro cewa Shugaban kasar ya yi jaje ga iyalai da yan uwan wadanda suka rasa ransu, inda yayi masu fatan samun rahmar Ubangiji. Ya kuma yi ma wadanda suka samu rauni fatan samun lafiya cikin gaggawa.

Buhari yayi jaje ga iyalan wadanda rushewar ginin Lagas ya cika da su
Buhari yayi jaje ga iyalan wadanda rushewar ginin Lagas ya cika da su
Asali: UGC

Shugaba Buhari ya kuma yi jaje ga gwamnati da mutanen jihar Lagas masu halin kirki, sannan ya sha alwashin cewa gwamnatin tarayya za ta bayar da tallafi kamar yadda jihar ka iya bukata.

KU KARANTA KUMA: Za ayi bala'i idan ku ka yi yunkurin magudi a zabukan da za a maimaita - Gargadin 'yan majalisa ga INEC da APC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wani gini mai hawa ukku da ke yankin Itafaji, tsibirin Legas ya rubza a ranar Laraba, lamarin da ya haddasa tashin hankali da rudani tsakanin al'ummar da ke zaune a kusa da ginin.

Channels TV ta ruwaito cewa akwai wata makarantar Firamare da ke a hawa na ukku na ginin, inda ake tsammanin daliban makarantar sun mutu, yayin da wasu har yanke ke a cikin ginin ba tare da samun hanyar fita ba. Akalla dalibai 70 suka ke cikin makaratar amma zuwa yanzu, an ceto yara uku.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel