Atiku ya cigaba da fafutuka, wata rana zai samu mulki inji Fasto Kasali

Atiku ya cigaba da fafutuka, wata rana zai samu mulki inji Fasto Kasali

- Muhideen Kasali yayi kira ga Atiku Abubakar cewa ka da ya karaya

- Shehin Malamin yace wata rana Atiku zai iya zama Shugaban kasa

Wani babban Malamin kirista mai suna Muhideen Kasali, ya bayyana cewa nan gaba Atiku Abubakar zai samu mulkin kasar nan. Malamin ya fadawa ‘dan siyasar cewa sam ka da ya karaya wajen neman mulkin Najeriya.

Muhideen Kasali ya fito yana cewa akwai alamun da ke nuna lallai ‘dan takarar shugaban kasar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP a zaben bana watau Alhaji Atiku Abubakar zai samu mulkin Najeriya da ya dade yana hari.

KU KARANTA: Akuya mai shekara 3 a Duniya ta zama Kantoma a Amurka

Atiku ya cigaba da fafutuka, wata rana zai samu mulki inji Fasto Kasali
An bayyanawa ‘Dan takarar PDP Atiku cewa zai samu mulki
Asali: Facebook

Atiku ya sha kasa ne a zaben 2019 a hannun Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC mai mulki. Tuni kuma ‘dan takarar ya sheka kotu inda yace fau-fau ba zai amince da sakamakon zaben ba yana kukan an yi magudi.

Babban Faston na cocin Hour of Mercy Prayer Ministry Worldwide (Watau Alaseyori) ya nunawa fitaccen ‘Dan siyasar cewa akwai alamun nasara nan gaba a tattare da takarar da yake yi na samun mulki, idan har ya dage.

Wannan Fasto yake cewa nan gaba kadan, za a iya jin Atiku ya zama shugaban kasa idan Allah ya kai mu zaben 2023, inda za a sake gwarawa. Malamin addinin ya nuna cewa shekarun Atiku ba za su kawo masa cikas a zaben ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel