Buhari ya amince da kashe Yuro miliyan 64.75 domin kawo ruwa Kano

Buhari ya amince da kashe Yuro miliyan 64.75 domin kawo ruwa Kano

A yau, laraba, ne majalisar zartar wa ta kasa (FEC) ta amince da kasha zunzurutun kudi da yawan su ya kai Yuro miliyan 64.75 domin wadata jihar Kano da ruwa.

Ministar kudi, Zainab Ahmed, ce ta bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa jim kadan bayan kamala taron na FEC da shugaba Buhari ya jagoranta.

Ta ce aikin, da za a dora wa gwamnatin jihar Kano alhakin kula da shi, zai inganta rayuwar jama’ar jihar Kano.

A zaman ta na yau, FEC ta amince da kasha kudi har Yuro 64,750,000 domin fara aikin wadata jihar Kano da ruwa.

“Idan aka kammala aikin, zai inganta rayuwar mutane miliyan 1.5 da ke zaune a yankunan karkara.

“Za a kasha kudaden ne wajen bunkasa cibiyoyin samar da ruwa da kuma gina wasu sabbi domin ganin dumbin al’ummar jihar Kano sun samu wadatar ruwa.

Buhari ya amince da kashe Yuro miliyan 64.75 domin kawo ruwa Kano
Taron majalisar zartar wa
Asali: Facebook

“Ma’aiktar albarkatun ruwa ta jihar Kano ce za ta dauki alhakin kula da aikin.

“Sabbin cibiyoyin da injinan da za a kafa a cibiyar za su kasance na aro ga gwamnatin jihar Kano a kan wasu sharuda,” a cewar minister.

Zainab ta kara da cewa wata kungiyar kasar Faransa ce za ta bayar da rancen kudin a kan sharadin dora kaso 1.02 a kan adadin kudin da za a biya cikin shekaru 20.

DUBA WANNAN: Sunaye: Buhari ya nada manyan darektocin hukumar NSIA

Fiye da ministoci 28 ne su ka halarci taron FEC na farko tun bayan kamala zabukan shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya da na gwamnoni da mambobin majalisar dokokin jihohi.

Mataimakin shugaban kasa; Yemi Osinbajo, sakataren gwamnati Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa; Abba Kyari, shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya; Winifred Oyo-Ita da mai bawa shugaban kasa a bangaren tsaro; Babagana Monguno, sun halarci taron FEC na yau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel