Za a ga alfanu sosai tattare da kokarinmu – Shugaba Buhari

Za a ga alfanu sosai tattare da kokarinmu – Shugaba Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta na ganin ta gyara sannan ta dawo da tarin asarar da kasar ta fuskanta

- Buhari ya ba da tabbacin cewa za a ga alfanu sosai tattare da kokarin da gwamnatinsa ke yi

- Yace Najeriya na iya bakin kokarinta, don ganin mun inganta abubuwa da dama, kara da cewa gwamnati na kokarin daukaka sunan kasar, a cikin gida da kuma waje

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta na ganin ta gyara sannan ta dawo da tarin asarar da kasar ta fuskanta, “sannan kuma za a ga alfanu sosai tattare da kokarinmu.”

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar jakadai, wadanda suka zo fadar Shugaban kasa Abuja domin yi masa murnar samun tazarce.

Za a ga alfanu sosai tattare da kokarinmu – Shugaba Buhari
Za a ga alfanu sosai tattare da kokarinmu – Shugaba Buhari
Asali: Facebook

Yace Najeriya na iya bakin kokarinta, “don ganin mun inganta abubuwa da dama,” kara da cewa gwamnati na kokarin daukaka sunan kasar, a cikin gida da kuma waje.

Shugaba Buhari yace gwamnati bata da wani uzuri idan har bata kulaa da jakadantaa ba a tashoshinsu daban-daban.

Ambasada Ashimiyu Olaniyi, wanda yayi Magana a madadin tawagar, yace zabar Shugaban kasa da aka yi a 2015 da kuma tazarcen da yayi ci gaba ne ga lamuran kasar.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Umahi zai koma APC kafin 29 ga watan Mayu – Sanata Ugbuoji

Ya kara da cewa za a dunga tuna Shugaban kasar a matsayin jigon siyasa da baya sanya baki a lamuran da suka shafi harkokin siyasar jiha.

Sun kuma jinjinawa Shugaban kasar akan tarin nasarorin da gwamnatinsa ta samu kama daga tattalin arziki, tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel